• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Ya Kammala Biyan Bashin Ma’aikata Fiye Da Naira Biliyan 9

by Leadership Hausa
1 year ago
gwamna

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya kammala biyan bashin haƙƙin ma’aikatan da suka bar aiki na shekara da shekaru, tun daga shekarar 2011, wanda ya kama Naira 9,357,743,281.35.

Idan dai za a iya tunawa, tun a watan Faburairun nan da ya gabata ne gwamnan ya amince da a fara biyan basukan na Garatutin tsoffin ma’aikatan.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa gwamnatin Zamfarar ta riga ta kammala biyan bashin Naira 4,860,613,699.22 rukuni-rukuni 9.

Haka kuma sanarwarta ce an biya tsaffin ma’aikatan Ƙananan Hukumomin jihar bashin su na Naira 4,497,129,582.13.

  • Abubuwan Da Ba A Sani Ba Game Da Sabon Harin Bam Na Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Idris ya ce: A jajircewarsa na ganin ya inganta aikin gwamnatin jihar Zamfara, a watan Faburairu Gwamna Lawal ya ƙaddamar da wani kwamitin da zai tantance duk ilahirin tsaffin ma’aikatan jihar da ba a biya su haƙƙoƙin su ba, tun daga shekarar 2011.

“Ya zuwa yanzu, cikin mutum 3,880 da aka tantance, mutum 2,666 sun karɓi haƙƙoƙin su, wanda ya kai ma Naira 4,860,613,699.22, daga cikin basukan da aka biyo gwamnatocin baya. An biya waɗanda suka bar aiki daga shekarar 2015 zuwa 2024.

“A ɗaya ɓangaren kuma, mutum 3,840 cikin ma’aikatan Ƙananan Hukumomi da Malaman Firamare 4,804 da aka tantance sun karɓi haƙƙoƙin su a rukunai 9, wanda ya kai ma kuɗi Naira 4,497,129,582.13. Haƙƙoƙin barin aiki na Garatuti da Ƙananan Hukumomi ke bi ya kai ma Naira 5,688,230,607.20, wanda yanzu haka an biya Naira 4,497,129,582.13. Waɗanda suka bar aiki a tsakanin shekarun 2011- 2021 ne suka amfana.

“A taƙaice dai, ya zuwa yanzu gwamnatin jihar ta biya Tsoffin ma’aikatan jiha da na Ƙananan Hukumomi da ya kai ma Naira 9,357,743,281.35 daga baussukan Naira 13,784,179,513.80 da tsaffin ma’aikatan suka biyo, wato Mutum 6,506, cikin mutum 8,684 da aka tantance. Su ne kuma waɗanda suka bar aiki a tsaknin shekarun 2011- 2024.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Thomas Etuh: Gwarzon Ɗan Kasuwa Na 2025

October 25, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)
Manyan Labarai

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Next Post
Alakar Arsenal Da ‘Yan Wasa Bakaken Fata

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025

Gwamnatin Katsina Ta Ƙara Samar Da Dakarun Tsaro 200 Domin Maganace Ta’addanci

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.