Connect with us

LABARAI

Gwamna Kashim Shettima Ya Rushe Kwamishinoninsa

Published

on

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya rusa baki dayan kwamishinonin sa, da yammacin ranar Talata.

A hannu guda kuma, wannan shi ne karon farko, bayan sake zaben sa karo na biyu, a cikin watan Mayun 2015, kana karo na biyu- a cikin shekaru 7 yana mulkin jihar.

Sanarwar rusa majalisar zartaswar ya zo ne ta bakin sakataren gwamnatin jihar Borno, Alhaji Usman Jidda Shuwa, inda ya bayyana cewa Gwamnan ya dauki matakin ne bisa damar da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bashi.

A madadin Gwamnan Shettima- sakataren gwamnatin jihar Borno ya mika matukar godiya dangane da hidimta wa jihar tare da yiwa tsuffin kwamishinonin fatan alheri dangane da abinda suka saka a gaba, a rayuwar su.

“Maigirma Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya dauki matakin bisa ikon da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bashi; sashe na 192 tare da karamin sashe na 2, wanda aka yiwa gyaran fuska- wajen rusa majalisar zartaswar jihar”. Inji shi.

Bugu da kari kuma, a cikin sanarwar, sakataren gwamnatin- Usman Jidda, ya umurci tsuffin kwamishinonin da cewa su gaggauta damka tafiyar da lamurran ma’aikatun ga sakatarorin din-din-din a ma’aikatun, ranar Jumu’a; 28 ga watan Satumba 2018, ko kafin ranar.

Har wa yau kuma, sakataren gwamnatin jihar Borno ya bayyana cewa za a sake nada majalisar zartaswar, a duk lokacin da ya kamata.

 

 
Advertisement

labarai