Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ziyarci ƙauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Kauran Namoda domin jajanta wa iyalan mutane 38 da ‘yan bindiga suka kashe kwanan nan.
Gwamna Lawal ya ce Allah zai tona asirin masu hannu a waɗannan mummunan hare-hare.
- ’Yansanda Sun Kama Mutum 2 Da Bindigogi Da Alburusai A Filato
- Gwamna Sule Ya Ziyarci Gidan Yarin Keffi Bayan Tserewar Fursunoni 16
Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Banga, Sakajiki, Kuryar Madaro, Maguru, da Tambarawa, duk a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda.
A yayin ziyarar, gwamnan ya tabbatar wa al’ummar yankin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da dukiyoyinsu.
Ya yi Allah-wadai da hare-haren, inda ya bayyana cewa manufar ‘yan bindigar ita ce tsoratar da mutane.
“Na zo Banga domin jajanta muku bisa wannan mummunan hari. Lokacin da abin ya faru bana nan, sai na umarci mataimakina ya jagoranci tawaga ta musamman domin yi muku ta’aziyya.
“Na dawo Gusau jiya, kuma abu na farko da na fifita yau shi ne zuwa nan da kaina. Gwamnati za ta ƙara ƙoƙari wajen yaƙar ‘yan bindiga,” in ji shi.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya ɗauki matakaki a kan waɗanda suka aikata wannan kisan gilla, sannan ya roƙi jama’a da su ci gaba da yin addu’a domin kawo ƙarshen duk wata ɓarna a Zamfara.
Sarkin Kauran Namoda, Dokta Sunusi Ahmad Rashad, wanda ya raka gwamnan, ya yaba masa bisa saurin ɗaukar mataki bayan faruwar lamarin.
“Wannan ziyara tana da matuƙar muhimmanci ga mutanen da abin ya shafa. Muna godiya, kuma Allah Ya ci gaba da maka jagoranci,” in ji shi.
Gwamna Lawal ya kuma yi alƙawarin inganta ayyukan more rayuwa a yankunan, kamar hanyoyi, wutar lantarki, ruwan sha, da sauransu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp