Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya kammala rangadin kananan hukumomi 34 na jihar inda ya bude wasu ayyukan da gwamnatin sa ta aiwatar da kuma wadanda shugabannin kananan hukumomi suka yi tare da dora harsashin wasu ayyukan.
Rangadin dai Radda ya kwashe kimanin kwana tara yana gudanarwa ya dauki hankali so sai musamman ‘yan adawa inda suka bayyana cewa yakin neman zabe ne yake yi a fakaice.
Barista Mustapha Shitu mashawarcin jam’iyar adawa ta ADC ya bayyana cewa babu abinda gwamnan Dikko Radda ke yi sai yakin neman zaben ta sigar dibara da wasa da hankali al’umma.
- Yadda Gwamna Raɗɗa Ya Yi Rangadi Ga Dukkanin Ƙananan Hukumomin Jihar Katsina
- Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro
Jam’iyyar adawa ta ADC ta dage cewa babu wani rangadi da bude ayyuka yakin neman zabe ne aka fara saboda gwamnati ta lura al’umma ta juya mata baya.
To, sai dai gwamnan da kansa ya bayyana cewa yanzu ba lokacin yakin neman zabe, inda ya yi kira ga ‘yan siyasa da su gu ji duk wani abu da zai alakanta su da batun siyasa.
Gwamnan dai ya fara wannan rangadi a shiryar Funtua inda ya kwashe kwanaki uku yana bi kananan hukumomi domin duba irin ayyukan da shugabannin kananan hukumomi suka asassa da kuma wanda shi ya aiwatar.
Wani abu da ya dora yatsan zargin akan wannan rangadi na gwamna Radda shi ne taron masu ruwa da tsaki na kowace karamar hukumar da ya ziyarta, inda ‘yan adawa ke cewa, wayan aci ne wai an kori kare.
Batutuwan da suka dabaibaye wannan rangadi na gwamna Radda sun hada da ganawa da jama’a musamman ‘ya ‘yan jam’iyyar APC da suka dadai ba su hadu ba.
Kazalika gwamnan Radda yana kai ziyarar ban girma ga masu rike da masarautar gargajiya musamman hakimai na kowace karamar hukuma kafin ya gana da masu ruwa da tsaki sannan ya wuce wajen taron domin kaddamar da ayyukan tallafi.
Wasu kananan hukumomin an ga yadda suka yi kokari wajen gwangwaje al’ummar su da kayan arziki wasu kuma ba yabo ba fallasa, wasu kuma babu wani abin azo a gani.
A karamar hukumar Batsari kuwa an iske shugaban karamar hukumar Hon. Munnir Mu’azu ya yi runton aiki inda ya kasa yin komi daga karshe ya buge da maida ayyukan tsohon shugaban karamar hukumar zuwa na shi.
Duk da haka, wasu kananan hukumomi irin su Safana da Jibia da Charanchi da Mani da Dutsi da Musawa da sauran su, sun yi namijin kokari wajen gwangwaje al’ummar su da ayyuka.
Ya kara da cewa yana fatan kayayyakin da aka rabawa al’umma na tallafi zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki musamman masu kananan sana’o’i a yankunan karkara.
Daga cikin abubuwan da aka samarwa al’umma sun hada da motoci da mashina da kekunan dinki da kudadai da injinan markade da na faci da sauran kayayyakin more rayuwa.














