Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya buƙaci a hanzarta kammala shari’o’in fursunonin da ke tsare a Gidan Gyaran Hali na Keffi.
Ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ziyarci gidan yarin a ranar Laraba, bayan fursunoni 16 sun tsere.
- Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwamnan Zamfara
- 2027: Jagororin APC Na Kudu-maso-Yamma Sun Amince Da Tinubu Ya Sake Tsayawa Takara
Yawancin fursunonin da ke zaune a gidan yarin suna da shari’a ne a kotunan Abuja.
Gwamna Sule ya ce hanzarta shari’o’insu zai taimaka wajen rage cunkoso a gidan yarin.
Ya kuma shawarci fursunonin da su kasance masu kyawawan halaye tare da bin doka.
Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da hukumomi masu ruwa da tsaki domin hanzarta shari’o’i da kuma rage cunkoson gidan yarin.
A lokacin ziyarar, ya lura da cewa yawancin fursunonin na zaune a ƙasa babu katifa.
Don inganta rayuwarsu, ya umarci a samar musu da katifu 500.
Gwamna Sule ya yaba wa jami’an gidan yari da sauran jami’an tsaro saboda sake kama wasu daga cikin waɗanda suka tsere.
Ya kuma roƙi jama’a da su kasance cikin shiri su kuma sanar da hukumomin tsaro idan sun ga wani mai kama da wanda ake nema.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp