Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ESK ya nuna matukar damuwarsa a bisa yadda wasu ‘yan jarida ke amfani da kafafen sadarwarsu wajen cin zarafin shuwagabanni a lokuta mabambanta. A cewarsa, ba ya daga cikin tsarin gudanarwa na aikin jarida. Gwamnan wanda ya nuna damuwar tasa a sa’ilin da sabbin shuwagabanin kungiyar ‘yan jarida reshen jihar Bauchi suka kai masa ziyara a gidan gwamnatin jihar a ranar Talatar da ta gaba.
Gwamnan ya kara da cewa, aikin ‘yan jarida ne su tabbatar da bayyana wa duniya gaskiya ba tare da nuna son-kai ko bangaranci ba. “Ba wai a kan Muhammad Abubakar ba kadai aikinku ne ku tabbatar da kun fada wa jama’a gaskiya, bai kamata dan jarida ya zama daga cikin wani bangare ba, abun da ya hau kanku shi ne ku bada labaranku a kan gaskiya ku fadi gaskiya a kan kowa”. In ji gwamnan.
A cewasa, “Ina son ya zama an sabunta alakar da ke tsakanin gwamnatin Bauchi da kuma kungiyar ‘yan jarida, ina godiya ga Allah da ya sanya a daidai lokacin da kuka zo ziyarar ga shi mun samu sabon mai tallafawa kan yada labarai, yana da kyau a samu kyakkyawan tsari domin al’ummar Bauchi suna bukatar sanin halin da jihar ke ciki”.
Ya ci gaba da cewa, hakkin ‘yan jarida ne su kasance tare da gwamnatin domin fitar wa jama’a halin da jihar ke ciki, ya bayyana cewar idan wasu na yada jita-jita a gefen titi hakkin ‘yan jarida ne su fito fili su bayyana wa jama’a mene ne gaskiyar magana.
Makama Babba na farko ya bai wa ‘yan jaridan dama da cewa su je su binciki ayyukansa da abubuwan da suka shigo cikin jihar tun lokacin da ya kama mulki, tare da cewa idan duniya ba ta jinjina masa kan biyan albashi ba to bai kuma kamata a kushe shi ba.
Gwamnan ya nuna sha’awarsa na aiki tare da ‘yan jarida da kuma shawo kan matsalolin da suke jibge domin a hada kai don yin hidima wa al’umman jihar Bauchi. Daga karshe dai gwamnan Bauchi ya sha alwashin cika wa ‘yan jarida dukkanin bukatun da suka gabatar masa, ya ce kuma zai je da kansa domin gane wa idonsa abubuwan da suke neman garambawul a sashin jarida a jihar tasa.
A nasa jawabin, sabon shugaban kungiyar ‘yan jaridan ta kasa reshen Jihar Bauchi Malam Ibrahim Muhammad Malam Gobe, ya bayyana cewar sun kawo ziyarar ne a bisa al’ada da zarar an gudanar da zaben kungiyar sabbin zababbun jagororin sukan kai ziyara wajen gwamnati domin sanayya.
A karshe, sabon shugaban kungiyar, kira ya yi ga dukkanin mambobinsa da su yi aikinsu da kwarewa domin tafiyar da komai yadda ya dace.