Khalid Idris Doya" />

Gwamnan Binuwai Bai Fice Daga APC Ba, Inji Wambai

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa a shiyyar Arewa ta Tsakiya, Alhaji Suleiman Wambai, ya bayyana cewar gwamnan jihar Binuwai Samuel Ortom bai fice daga jam’iyyarsu ta APC ba.
Wambai wanda ya bayyana hakan a lokacin da ke tattaunawa da ‘yan jarida a garin Lafia a Larabar nan, ya ce, gwamnan har zuwa yanzu bai rubutu wa uwar jam’iyyar a rubuce kan cewar ya fice daga jam’iyyar ba, ko kuma niyyarsa ta ciewa daga jam’iyyar, ya kara da cewa babu wani sadarwa a tsakaninsu kan wannan zancen, don haka ne ya bayyana cewar a matsayinsu na jam’iyya basu da masaniya, don haka har yanzu Ortom dan APC ne a wajensu.
Ya ce, “mun ga labarai a gidan jaridu daban-daban, da ke cewa wai gwamnan Binuwai ya fice daga APC a sakamakon jar kati da aka bashi a jam’iyyar. Tunin uwar jam’iyyarmu ta kasa ta tsunduma cikin lamarin jam’iyyar a jihar ta Benue domin shawo kan lamarin,” In ji shi.
Ya bayyana cewar jam’iyyar ta APC za ta yi aiki kafa da-kafa da domin ganin jam’iyyar ta nausa gaba domin samun nasara a babban za ben 2019 da ke tafe musamman a shiyarsa da ke jagoranta.
Idan dai baku mance ba, gwamnan jihar ta Binuwai Samuel Ortom ya shelanta ficewarsa daga jam’iyyar a wajen bikin rantsar a mai bashi shawara kan har ko kin kananan hukumomi, inda ya ce ya dau matakin hakan ne a sakamakon jar kati da jam’iyyar ta bashi.

Exit mobile version