Idris Aliyu Daudawa" />

Gwamnan Borno Ya Yi Wa Likitan Munguno Sha Tara Ta Arziki

Borno

Gwamnan Jihar Barno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya amince da cewar a biya Naira miliyan 13.9 da kuma kyautar sabuwar  mota ga wani likita mai shekaru 65, dan asalin Jihar Jihar Ogun, wanda ke zaune a cikin Babban Asibitin da ke Monguno kuma ya ci gaba da ba da kulawa ga marasa lafiya, wannan ma har ya hada da lokacin da garin ya fuskanci mafi munin barazanar rashin zaman lafiya da kuma tashin hankali, daga kungiyar Boko Haram ta kawo a shekarun baya.

Dokta Isa Akinbode, dan asalin Jihar Ogun ne, ya yi  karatunsa na sashen Likita a Jami’ar Maiduguri, bayan ya yi wa kasa hidima kuma sai ya fara yi aikin a karkashin gwamnatin Jihar Borno, ya yi  kuma aiki ne  har na tsawo shekaru 22 kafin ya yi ritaya a shekarar 2016 a babban Asibitin Monguno.

Bayan ya yi ritaya daga aiki ne likitan duk kuwa da akwai rahotanni da suka ce sau daya ne kungiyar Boko Haram ta sace shi kuma ta sake shi a Monguno, amma duk da hakan ya ci gaba da kasancewa a babban asibitin da ke Monguno. Wannan kuma ba domin komai ba sai saboda sha’awar sa ta kulawa da marasa lafiya, a cikin irin ziyarar da Gwaman Kashim Shettima ya kai a lokacin, daya daga cikin ziyarar da ya kai Monguno, ya umarci jami’an ma’aikatar lafiya ta jihar da su sa Akinbode a matsayin ma’aikacin kwangila.

Ganin shi tsohon gwamman ya kammala wa’adinsa, sai su ma’aiakatan day aba umarni, suka yi biris da maganar tasa, ma’ana basu dauki wani mataki ba, duk kuwa da yake shi ba wai barin aikin ya yi ba ci gaba ya yi da aikin.

Ranar Jumma’a ta wannan makon da muke ciki wanda shekaru biyar ke nan sai kuma ga Gwamna Zuluminda ya bayar da umarnin a biya Dokta. Hakkokin sa. Bugu da kari kuma Gwamnan ya ba shi kyautar mota kirar Toyota Highlander a matsayin kyauta ga Dakta Akinbode saboda ayyukansa ga mutanen Borno da suka karbi bakuncin sa.

Exit mobile version