Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kafa kwamitin mutane 10 domin bincikar hare-haren da ake ta fama da su a jihar.
An ƙaddamar da kwamitin ne a Jos, kuma an ba su aikin gano adadin al’ummomin da aka kai wa hari tun daga shekarar 2001 zuwa yanzu, yawan mutanen da suka mutu, irin ɓarnar da aka yi, da kuma waɗanda ake zargin suna da hannu a lamarin.
- DSS Ta Cafke ÆŠan Bindiga Yayin Da Yake Shirin Tafiya Aikin Hajji A SakkwatoÂ
- NiDCOM Ta Ceto ‘Yan Nijeriya 13 Da Aka Yi Safarar Zuwa Ghana Da Mali
Gwamna Mutfwang ya ce manufar kwamitin ita ce gano musabbabin matsalolin tsaro da kuma bayar da shawarwari domin samun zaman lafiya mai É—orewa.
Kwamitin zai kuma binciki hanyoyin da masu hare-hare ke bi a jihar, tare da bayar da shawarwari kan yadda za a hana su.
Shugaban kwamitin, Manjo-Janar Rojas Nicholas (mai ritaya), ya ce za su yi aiki da adalci da gaskiya domin fitar da rahoto mai inganci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp