Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bai wa kungiyar Kiristoci ta kasa a jihar (CAN) tallafin naira miliyan 25 domin gina masaukin baki na kungiyar tare da karin wasu naira miliyan 15 don shingace cibiyar da sauran ayyuka.
Tallafin kudin na zuwa ne a lokacin da mambobin Ƙungiyar Kiristoci a Jihar Gombe suka kai wa gwamnan ziyarar bangirma ta sabuwar shekara.
Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya, CAN reshen Jihar Gombe, Rev. Fr. Joseph Alphonsus Shinga yayin ziyarar ya ce mabiya Addinin Kirista a jihar su na alfahari da irin ayyukan da Gwamnan yake yi a fannin samar da ababen more rayuwa a sassa masu muhimmanci na tattalin arzikin jihar, yana mai jaddada cewa idan ya sake samun dama a karo na biyu, jihar za ta shiga wani sabon salo na ci gaba da wadata.
Shinga ya kuma yaba da irin goyon bayan da Gwamna ke bai wa kungiyar CAN, yana mai cewa gwamnan yana bin Kiristocin jihar bashi na ci gaba da goyon bayan manufofi da shirye-shiryen gwamnatin sa, saboda halayen sa ababen koyi.
Ya godewa Gwamnan bisa daukar nauyin Kiristoci 33 da suka yi aikin ibada a kasar Isra’ila da Jordan a 2022, ya kuma buƙaci a ci gaba da wannan tallafi.
Sai ya yi kira ga Gwamna Inuwa Yahaya, ya taimakawa kungiyar wajen samar da ruwan sha ga cibiyar ta CAN, ya kuma bukaci tallafin kudi don gina masaukin baki na kungiyar wanda gwamnatinsa ta taimaka wajen ginata ta hanyar tallafin daya bayar a baya.
A nasa jawabin, Gwamna Inuwa ya godewa al’ummar Kiristocin jihar bisa hadin kan da suke bai wa jihar wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman idan aka kwatanta da kalubalen tsaron da jihohin dake shiyyar Arewa maso Gabas ke fuskanta da sauran su.
Ya ce saboda zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ake samu a jihar ya sa gwamnatinsa ke iya gudanar da ayyuka don tabbatar da ci gaban al’umma da bunkasa tattalin arziki da ababen more rayuwa, don haka ya bukaci al’ummar jihar su zamto masu kishi da kiyaye duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa, a yayin bikin Kirsimeti, gwamnatin sa ta bada tallafin kuɗi fiye da Naira miliyan 90 domin tallafawa al’ummar Kirista a jihar wajen gudanar da bukukuwan su cikin sauƙi duba da halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki.
Ya kuma sanar da kyautar Naira miliyan 10 ga Kiristocin a matsayin goron sabuwar shekara, inda aka ware Naira miliyan 5 ga mata da kuma wasu miliyan biyar ga maza.
“Hakazalika dangane da bukatar ku ta tallafi a harkar samar da ruwan sha a cibiyar ta CAN, kamar yadda kuka sani muna kan aikin fadada shirin samar da ruwan sha na Gombe, kuma na yi imanin cewa kwanan nan kun ga Ministan Albarkatun Ruwa ya zo ya kaddamar da aikin inda gwamnati ke kashe fiye da Naira biliyan 11.68 don samar da ruwan sha ga al’ummar da aka yi watsi da ita, musamman ma yankunan Tunfure har zuwa cibiyar taro ta ƙasa da ƙasa da kewaye”.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi amfani da damar wajen yin kira ga al’ummar jihar su karbi katin zaben na dindindin don yun amfani da ‘yancin su su zabi ‘yan takaran da suke so.