Daga Khalid Idris Doya,
Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa, gwamnatin sa za ta ci gaba da kawo tsare-tsaren da za su dakile yawaitar rashin ayyukan yi da talauci da ayyukan bata gari a fadin jihar.
Ya bayyana cewa, a duniya an amince da harkokin kungiyoyi a matsayin hanyar cin gajiyar harkokin walwala da tattalin arziki ga al’umma.
“Bincike ya yi nuni da cewa, kungiyoyi a nahiyar Afirka su na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa walwala da ci gaban yankunan karkara da birane.”
Gwamnan ya ce tun lokacin mulkin mallaka, harkokin kungiyoyi na kan gaba wajen bunkasa tattalin arziki da walwala, wanda ya ce ko jihar Gombe a shekarun baya, kungiyoyi sun taka muhimmiyar rawa a bangaren kasuwanci da samar da abinci da sauran kayayyakin noma da ake sarrafawa, wadanda suka kasance hanyoyin samun arziki da kyakkyawan rayuwa.
“Don cimma wannan buri, gwamnati ta hada hannu da gidauniyar kwararru a sashin bunkasa harkokin kungiyoyin gamin kai, don taimakawa wajen kula da shirin, baya ga sashi da ake kokarin samar wa a ma’aikatar bunkasa karkara da kungiyoyin gamin kai ta jihar Gombe don ci gaba da aikin da kula da shirin.”
Ya kuma kara da cewa, don rage matsalolin da za a iya fuskanta, shirin zai hada hannu da shirye-shiryen gwamnatin tarayya makamantan sa, da suka hada shirin tallafi na Anchor Borrowers da na Nirsal dana kungiyar bunkasa kayayyaki, da zummar samar wa da sarrafa kayayyaki tare da bunkasa tattalin arziki da ci gaban harkar noma, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki da su yi amfani da wannan tsari don dakile matsalar rashin ayyukan yi da talauci da ayyukan barna.
Tun farko da yake jawabi, Kwamishinan bunkasa karkara da kungiyoyin gamin kai, Honorable Usman Muhammad Jahun Biri ya bayyana cewa, an dauri aniyar shirin ne a shekarar 2020 wadda majalisar dokokin jihar Gombe ta amince da shi don sake farfado da harkokin kungiyoyi a jihar.
Shi ma, shugaban tawagar gidauniyar kwararru a sashin bunkasa kungiyoyin gamin kai, Jonathan Dangwaram ya bayyana cewa, yadda gwamnan yake maganar shirin, ya nuna bukatar sa na sauya rayuwar al’ummar jihar.
Ya ce gidauniyar ta daura aniyar farfado da harkokin kungiyoyin gamin kai wadanda suka yi aiki ga tsohuwar Gombe da yanki arewa maso gabas dama kasa baki daya.