Gwamnan Gombe Ya Sha Alwashin Kyautata Rayuwar Malamai Bisa Gudunmawarsu Ga Al’umma

Daga Khalid Idris Doya

 

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya jinjina wa Malamai a jihar Gombe da Nijeriya baki daya bisa gagarumar gudunmowa da sadaukarwar da suke yi ga ci gaban al’umma ta hayar bada ilimi da kyautata goben dalibai duk da irin kalubalen da ake fuskanta.

Advertisements

A wani sakon fatan alhairi da ya fitar dauke da sanya hannakun babban mai taimaka masa kan hulda da ‘yan jarida Alhaji Ismaila Uba Misili, kan ranar malaman ta bana, Gwamna Inuwa ya bayyana malamai a matsayin wasu rumbun ilimin da yara manyan gobe ke samun haske daga gare su a yayin da su ke girma.

Sai ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da walwala, ci gaba dama karfafa malaman Jihar.

Gwamnan sai ya bayyana taken ranar malaman ta bana wato “Malamai: jagorori a lokutan kalubale, don sake fasalin makoma al’ummah” da cewa ya zo akan gaba, yana mai cewa “Aikin ilmantarwa, reno da saita tunanin al’umma ka iya zama mai cike da kalubale, amma kuma yana daya daga cikin ayyuka mafiya kima da nagarta a duniya.

“Gwamnatinmu ta gano irin muhimmin rawar da malamai da aikin malanta ke takawa ga ci gaban al’umma, don haka zamu ci gaba databbatar da ba su horo, da kyautata walwalarsu dama samar musu da kayan aikin da ake bukata ciki har da na zamani don karfafa musu gwiwa da kwazo a dukkannin matakai.”

Ya ce gwamnatinsa ta karfafa alaka da hukumomi da kungiyoyin da suka dace ciki har da Hukumar Ilimin Bai Daya Daga Tushe UBEC, da Hukumar Samar da Ci Gaba ta kasar Amurka USAID dama kungiyoyin ciki da wajen kasar nan don sake farfado da sashin ilimi da bunkasa hazakar malamai don aiki mai nagarta.

Gwamna Inuwa ya ce dokar ta bacin da tun farko ya ayyana kan ilimi ya yi shi ne don tabbatar da nagartacciyar hanyar samar da kayan aiki da ma’aikata don sake farfado da sashin don kwalliya ta biya kudin sabulu.

 

Exit mobile version