Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi kira da Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar cewar ‘yan gudun hijira da suka kai 800,000, wadanda kuma suke a matsugunnai daban-daban wuraren da matsalar Boko Haram ta shafa, suna matukar bukatar abinci ba tare da bata wani lokaci ba.
Wannan bayanin na bukatar matakin gaggawa akan su ‘yan gudun hijira mai ba gwamnan shawara ne na musamman akan harkokin watsa labarai da sadarwa Malam Isa Gusau, ya bayyana haka a Maiduguri ranar Juma’a ta wannan makon da muke ciki na sabuwar shekara.
Gusau ya bayyana cewar gwamnan ya mika tasa bukatar nea wata takarda daya gabarta lokacin daya kai ziyara a hedikwatar Hukumar dake Abuja ranar Alhamis, inda ya bayyanawa shi Shugaban Hukumar bukatar ta masu gudun hijira da suke garuruwa sha daya.
Mai ba gwamnan shawara ya ce “Gwama Zulum a takardarin ya sanar da Shugaban Hukumar ritaya ABM Muhammadu Alhaji Mohammed akan ‘yan gudun hijira a, Monguno, Bama, Damboa, Gwoza, Dikwa, Gamboru, Ngala, Damasak, Banki, Pulka da Gajiram suna matukar bukatar samun kayayyakin abinci.”
Bugu da kari ya kara jaddada cewar “Zulum ya ce ita maganar taimakawa da abinci abu ne wanda ya dace a ci gaba da yin shi, saboda kuwa yawancin su ‘yan gudun hijirar sun ta’allaka ne da noma, wanda, a irin cikin mawuyacin halin da suke cike, yana da wuya su je gonakin su saboda gudunn hare- haren da ake akai masu.”
Ya ce Shugaban Hukumar ta NEMA ya ba shi gwamnan tabbacin cewar shi wannan agajin musamman na abinci abinda za a ci gaba da bayar da shi ne. Ya kuma nuna jin dadin sa akan yadda mulkin gwamnan na Borno yake kokarin kawo gyare- masu masu amfanar al’ummar jihar, ta tsare- tsaren cigaban daya zayyana.
Hakanan ma shugaban NEMA ya kara ba shi gwamna Bornon tabbacin cewar za su ba shi tainako, musamman ma bangaren ganin an samu cimma burin tsarin ci gaban jihar da zai shekara 25 da gwamnan ya bayyana.
Gwanan Bornon ma ya kai ziyara ma’aikatar harkokin waje inda ya sadu da Ministan Geoffrey Onyema, irin taimakon da gwamnatin tarayya zata yi akan ‘yan gudun hijira’yan Nijeriya, wadanda suke kasar Kamaru a shekaru shida da suka gabata.
Manema labarai sun bada rahoton cewar da akwai ‘yan gudun hijira’yan asalin Nijeriya fiye da 60,000 wadanda suke a matsugunnin su na Minawawo a Kamaru, wadanda kuma suke ta jira na azo a dauke su.