Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq a ranar ma’aikata, ya gwangwaje manyan alkalan jihar da manyan motoci kirar Toyota Fortuner Jeep guda 11.
Alkalin alkalan jihar, Mai shari’a Abiodun Adebara, ya samu mota kirar Toyota Land Cruiser (2024) domin yin amfani a ofishinsa, a wani mataki na kara wa alkalan himma kan hidimar da suke yi wa jihar da kuma kasa baki daya.
- ‘Yar Sanda Da Wata Sun Shiga Hannu Kan Sato Yara 5 Daga Sakkwato
- Ba Za A Raba Ci Gaban Kasar Sin Da Gudunmuwar Mata Ba
A yayin gabatar da motocin a hukumance ga wadanda suka ci gajiyar a babbar kotun jihar, Ilorin, Mai shari’a Adebara ya bayyana cewa, a farkon watan Fabrairun bana, an ware motocin Toyota Fortuner Jeep guda biyar ga alkalan babbar kotun jihar daga cikin kudaden da gwamnatin jihar ta ware karkashin kasafin kudin 2023.
Adebara ya bayyana cewa, siyan sabuwar mota sharadi ne na nadin sabon alkali.
Ya bayyana cewa, karo na karshe da alkalan suka karbi motoci daga gwamnatin jihar shekaru takwas da suka gabata kenan baya ga alkalan da aka nada a shekarar 2020 kuma ya yaba wa Gwamna Abdulrazaq bisa yadda yake kula da harkokin shari’ar jihar.