Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika takardun dorewar aiki na dindindin ga sabbin malamai 400 da aka dauka domin koyar da lissafi a makarantun sakandaren jihar.
A cewar wata sanarwa daga mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya ce daukar malaman na da alaka kai tsaye da cike gibi a fannoni da ke shafar kwarewa da shirye-shiryen dalibai wajen neman ilimi da sana’o’i.
- Ƙungiyar IPOB Ta Yi Watsi Da Hukuncin Ɗaurin Rai-Da-Rai Ga Nnamdi Kanu
- Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Ƙaddamar Da Jakadun Wayar Da Kai Game Da Rigakafi
Ya bayyana cewa lissafi shi ne tushen kimiyya, fasaha, injiniya da kirkire-kirkire, kuma dole ne Jihar Kano ta gina tushen da ya dace domin iya yin gogayya yadda ya kamata a duniyar da ke dogaro da ilimi.
Gwamna Yusuf ya ce sabbin malaman za su inganta koyarwa, su kara kyautata sakamakon jarrabawa, tare da karfafa hanyoyin dalibai zuwa manyan fannoni na STEM.
Ya jinjinawa Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta Kano (KSSSSMB) bisa gudanar da tsarin daukar aiki cikin gaskiya da tasiri.
Gwamnan ya yi kira ga sabbin malaman da su koyar da kishin aiki, jajircewa da kwarewa, yana mai jaddada cewa dole su tabbatar da sun cancanci amincin da aka nuna musu.














