Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafen Al’umma da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar (PCACC), domin kammala wa’adinsa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa, babban sakataren yada labaran gwamnan jihar.
- Asamoah Gyan Ya Yi Ritaya Daga Kwallon Kafa
- Babu Kwamishinan Da Za A Rantsar Idan Bai Bayyana Kaddarorinsa Ba –Gwamnan Kano
Idan za a iya tunawa tsohon gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje ne ya dakatar da Muhuyi tare da tsige shi daga mukaminsa bayan majalisar dokokin jihar ta ce tana da shakku kan yadda yake gudanar da ayyukansa.
Muhyi ya kai tsohuwar gwamnatin jihar kara kotu kan neman wasu hakkinsa, inda kotun ta sahale masa aka biya sa.
Sanarwar ta bayyana cewa Barista Muhuyi zai koma kan aikinsa ne nan take.