Daga Muhammad Awwal Umar,
Gwamnan Neja Abubakar Sani Bello kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC a arewa ta tsakiya, ya kaddamar da sabunta rajistan ‘yayan jam’iyyar APC a yankin arewa ta tsakiya.
Gwamnan Wanda shi ne shugaban kwamitin sabunta rajistan ‘yayan jam’iyyar, ya sabunta rajistarsa a runfar zabe ta Alkali Mustapha da mazabar tsakiya da ke karamar hukumar Kontagora da jihar Neja domin ya tabbatar shirin sabunta rajistan ya kan kama a yankin.
Ya ce, aikin da ya karba a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne ya tabbatar aikin ya kai ga talakawa, yace dukkan ayyukan sabunta rajistan za a gudanar da shi ne a matakin runfunar zabe.
“A baya an gudanar da rajistan ‘yayan jam’iyyar ne a shekarar 2014 kuma mun samu ‘yan kalilan din jama’ar da suka bar jam’iyyar kuma mun samu jama’a da dama da suka shigo jam’iyyar.”
Ina da tabbacin wannan aikin ya samu amincewar shugaban riko na jam’iyyar ta kasa kuma wannan hanyar da aka dauko yana kan tsarin diimukuradiyya wanda bai sabawa tsarin jam’iyyar ba”.
Shugaban kwamitin ya bada tabbacin cewar ba wanda za a bari a baya wanda yace zasu cigaba da sanya idanu a duk kasar nan dan ganin an yiwa duk mai bukatar shiga jam’iyyar damar yin rajistan, ba tare da yin alfarma ga wani ko wata kungiya ba.
Ya ce, “a kowani lokaci sabunta rajistan zai cigaba. Sanin kowa ne za a tsayar da yin rajistan wata daya kafin zaben fidda gwani. Za a cigaba ba wanda za a bari baya za a tafi tare da kowa.”
A hannu daya, Sanata Osita Izunaso, kodineta sabunta rajistan a yankin arewa ta tsakiya wanda ke tare Sanata Domingo Obende shugaban kwamitin sanya ido a sabunta rajistan a jiha suna cigaba da sanya idanu akan kaddamar da shirin a Neja.
Sanata Izunaso ya tabbatar sabunta rajistan gwamna Abubakar Sani Bello a matsayin dan jam’iyyar.
Kan tsoron da ‘yayan jam’iyyar ke nunawa na alkawalin yiwa kowa rajistan, yace karin kayan aikin na tafe dan sabunta rajistan dukkan ‘yayan jam’iyyar.