Gwamnatin Jihar Neja ta yi Allah-wadai da sace ɗaliban makarantar St. Mary da ke Papiri a ƙaramar hukumar Agwara, inda Gwamna Muhammad Bago ya bayyana cewa har yanzu ba a tantance adadin yaran da aka sace ba. Ya faɗi hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a safiyar yau, inda ya ce lamarin ya sake tayar da hankalin gwamnati da al’umma gaba ɗaya.
Gwamnan ya ce tun da farko gwamnati ta samu bayanan sirri kan yiwuwar kai hari a yankin, wanda hakan ya sa ta dakatar da ayyukan ƴan kwangila tare da rufe makarantu don kare rayukan ɗalibai. Sai dai makarantar St. Mary ta ci gaba da buɗe makaranta ba tare da sahalewar gwamnati ba, lamarin da gwamnan ya ce ya saɓa wa umarnin tsaro da aka bayar domin kare lafiyar ɗalibai.
- Yadda Sojoji Suka Tarwatsa Haramtattun Matatun Mai 14 A Yankin Neja Delta
- Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja
A cewar Gwamna Bago, jami’an tsaro sun fara aikin ceto tun da labarin ya faru, kuma gwamnati na karɓar sahihan bayanai daga hukumomin tsaro domin tabbatar da komowar ɗaliban cikin ƙoshin lafiya. Ya ce ana cigaba da tunkarar lamarin cikin tsari da natsuwa domin ganin an fatattaki masu garkuwa da kuma kuɓutar da yaran.
Gwamnan ya yi kira ga shugabannin makarantu da su dinga bin umarnin jami’an tsaro ba tare da kaucewa wani mataki da zai sanya rayuwar ɗalibai cikin haɗari ba. Haka kuma ya umurci al’umma da su ƙwantar da hankalinsu tare da baiwa jami’an tsaro cikakken haɗin kai ta hanyar isar da bayanai da zasu yi amfani don hanzarta ceto ɗaliban da aka sace.














