Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya kaddamar da kwamitin da zai binciki wasu ayyukan da gwamnatin da ta shude ta Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta dauka yayin da yake kan mulki.
Ana sa ran kwamitin karkashin jagorancin tsohon Alkalin Alkalan Jihar Gombe, Mai Shari’a Muazu Abdulkadir zai gabatar da sakamakon bincikensa cikin wata biyu.
- Jihohin Da Aka Samu Mahajjata Masu Juna Biyu Za Su Fuskanci Hukunci – NAHCON
- Daidaita Farashin Canji Ya Fara Haifar Da Da Mai Ido A Nijeriya
Yayin rantsar da kwamitin binciken, Gwamna Aliyu ya bukace su da su gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada.
Gwamnan ya ce ya yanke shawarar kafa kwamitin binciken ne domin a samu biyan bukatun al’ummar jihar.
A jawabinsa yayin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan rantsar da shi, shugaban kwamitin, mai shari’a Muazu Abdulkadir Pindiga, ya bada tabbacin cewa kwamitin zai gudanar da aikinsa ba tare da tsoro ko fargaba ba.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da; Cif Jacob Ochidi SAN, Usman Abubakar, Lema Sambo Wali Esq, Alhaji Haliru Dingiyadi da Nasiru Mohammed Binji Esq.