Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya rattaba hannu kan rage ma’aikatun gwamnatin jihar daga 28 zuwa 16, don Farfado da tattalin arzikin Jihar.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis ta hannun mai magana da yawun gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris.
- Bikin Sallah: Dauda Lawal Ya Taya Musulmi Murna, Ya Nemi A Dage Da Addu’a
- ‘Yan Sa-Kai Sun Kashe Mutum 6 A Zamfara
Sabbin ma’aikatun da aka amince da su sun hada da ma’aikatar Noma, Kasafin Kudi da Kimiyya da Fasaha, Muhalli da Albarkatun Kasa, Kudi, Lafiya da Kasuwanci da kuma Ciniki da Masana’antu,
Sauran su ne Ma’aikatar Watsa Labarai da Gidaje da Raya Birane da Ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu sai ma’aikatar Al’amuran Addini da Ma’aikatar Harkokin Mata da ta Ayyuka da kuma ma’aikatar Matasa da Wasanni da ta Tsaron Cikin Gida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp