Gwamnatin Tarayya ta sanya wa’adin mako shida domin kammala aikin gina gidaje a Renewed Hope City da ke Kano, a wani mataki na gaggawa don rage gibin rashin gidaje a ƙasar. Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara wurin aikin, inda ya bukaci a kammala dukkan ayyukan cikin gida, lantarki, ruwan sha da sauran ababen more rayuwa kafin ƙarshen watan Agusta 2025.
Ko da yake an samu wasu ƙananan sauye-sauye a cikin zanen aikin, Ministan ya bayyana cewa an amince da su tun farko kuma ba su karya ƙa’ida ba. Ya yaba da jajircewar shugaban aikin a Kano, yana mai cewa hakan ne ke sa ci gaban aiki ya yi sauri—abinda yawancin ayyukan gwamnati ke rasaw a faɗin ƙasa.
- Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincikar Kwamishinan Sufuri Kan Karɓar Belin Dilan Ƙwaya A Kano
- EFCC Ta Kama Ɗaliban BUK 25 Kan Zargin Aikata Damfara A Intanet A Kano
Sai dai, akwai gagarumar matsala da ta shafi ingancin ababen more rayuwa. Wani sabon sashin hanya a cikin rukunin gidajen an lalata shi saboda manyan motocin dakon kaya da suka fi ƙarfin hanyar. Dangiwa ya bayar da umarnin gaggawa na sanya shingen ƙarfe da kuma gyaran hanyar da aka lalata. Wannan ya nuna cewa akwai gazawa wajen tsari da bincike tun da farko.
Aikin Renewed Hope City wani ɓangare ne na shirin gwamnati na samar da gidaje masu sauƙin kuɗi ga ‘yan Nijeriya musamman masu ƙaramin albashi. Taron ya samu halartar manyan jami’ai kamar ƙaramin Minista Yusuf Abdullahi-Attah, lamarin da ya ƙara nuna muhimmancin aikin a matakin ƙasa.
Sai dai, nasarar aikin ba zai dogara ne da wa’adi kaɗai ba—ya kamata a tabbatar da gaskiya wajen rarraba gidajen, da bayar da haya mai sauƙi, da kuma tsarin kulawa da zai tabbatar da inganci har bayan kammala aikin.
Idan aka aiwatar da wannan aiki yadda ya kamata, zai iya zama abin koyi a tsarin samar da gidaje a Nijeriya. Amma in aka bar shi ya faɗa cikin halin almubazzaranci da rashin kulawa da ya jima yana faruwa, to zai iya zama wani sabon abin misalin da ba zai amfani talaka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp