Gwamnatin tarayya ta ce ta bankado sunayen wasu hukumomi 15 da suka hada da mutane tara da wasu kamfanoni shida na Bureau De Change, da ake zargi da hannu wajen ba da kudade a ayyukan ta’addanci.
Sashen Kula Da Harkokin Kudi Na Nijeriya ne ya bayyana cikakken bayanin ci gaban, a cikin wani sakon email da ya aike wa wakilinmu, mai taken “Daidaikun mutane da hukumomi na ranar 18 ga Maris, 2024.”
- Wuraren Kiwo: Fulani Sun Yi Murna Da Matakin Shugaban Kasa – Ngelzarma
- Ɗaliban Jami’ar Jihar Nasarawa 2 Sun Mutu A Yayin Turmutsutsun Karɓar Abincin Tallafi
Takardar ta bayyana cewa kwamitin takunkuman na Nijeriya ya gana ne a ranar 18 ga Maris, 2024, inda aka ba da shawarar wasu mutane da hukumomi da a kakaba mata takunkumi biyo bayan shigar da suke yi wajen bayar da kudaden ta’addanci.
“Mai Girma Babban Lauyan Tarayya, tare da amincewar shugaban kasa, ya sanya sunayen mutane da hukumomi da za a amfata masu zuwa da aka sanya su a cikin jerin sunayen,” kamar yadda takardar ta karanta a wani bangare.
Daga cikin mutanen da aka bayyana sunayensu a cikin takardar akwai wani mawallafin da ke zaune a Kaduna, Tukur Mamu, wanda a halin yanzu gwamnatin tarayya ke shari’a bisa zargin taimakawa ‘yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a watan Maris din 2022.
A cewar takardar, Mamu “ya shiga harkar tallafa wa ayyukan ta’addanci ta hanyar karba tare da bayar da kudaden fansa kan kudi dalar Amurka 200,000 domin tallafa wa ‘yan ta’addar ISWAP domin sako mutanen da suka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna.”
Takardar ta ce daya daga cikin mutanen shi ne “wanda ake zargi da kai hari Cocin St. Francis Catholic Church Owo, Jihar Ondo a ranar 5 ga Yuni, 2022 da kuma Gidan Gyara Hali na Kuje, Abuja a ranar 5 ga Yuli, 2022.”
“(a) Ku gaggauta tare da ganowa gami da rufewa, ba tare da sanarwa ba, na duk wasu kudade, kadarori, da duk wasu albarkatun tattalin arziki na mutanen da hukumomin da ke hannunku sannan ku kai rahoto ga kwamitin sanya takuynkumi;
“(b) Kai rahoto ga kwamitin takunkumin duk wata kadara da aka rufe asusunta ko ayyukan da aka yi bisa ka’idojin haramcin.
“(c) Nan da nan ku shigar da Rahoton Mu’amala da ake tuhuma ga NFIU don karin bincike kan ayyukan kudi na irin wannan mutum.
“(d) Bayar da rahoto a matsayin Rahoton Mu’amaloli da ake tuhuma ga NFIU, duk shari’o’in da suka dace da ma’amalar kudi kafin ko bayan samun wannan Jerin sunayen.”
“(a) A rufe duk wasu kudade ko wasu kadarorin da ke hannun mutane da hukumomin da aka kebe, ba wai kawai wadanda ke da alaka da wani aiki, makirci, ko barazanar ta’addanci ko tallafin ta’addanci ba;
“(b) Rufe asusun kudade ko wasu kadarorin da ke da hadin gwiwa wajen mallakarsu ko sarrafawa, kai tsaye ko a kaikaice, ta mutane ko wasu da aka kebe;
“(c) Daskarar ko kuma rufe kudade ko wasu kadarorin da aka samu ko aka samu daga kudade ko wasu kadarorin da aka mallaka ko sarrafa su kai tsaye ko a kaikaice ta wasu mutane ko hukumomi da aka kebe; kuma
“(d) kudade ko wasu kadarorin mutane da hukumomin da ke aiki a madadin, ko kuma a jagorancin mutanen da aka kebe ko kungiyoyi.”
A cewar takardar, Mamu “ya shiga harkar tallafa wa ayyukan ta’addanci ta hanyar karba tare da bayar da kudaden fansa kan kudi Dalar Amurka 200,000 domin tallafa wa ‘yan ta’addar ISWAP domin sako mutanen da suka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna.”
Wani kuma an bayyana shi a matsayin “dan kungiyar ta’adda ta Ansarul Muslimina Fi Biladissudam, kungiyar da ke da alaka da Al-Kaeda a yankin Magrib.
“An gabatar da batun kuma an yi aiki a karkashin Muktar Belmokhtar, mai lakabi da ‘One Eyed Out’, wanda ya jagoranci Al-Murabtoun Katibat na AKIM a Aljeriya da Mali.”
NFIU ta ce mutumin “ya kware wajen tsara lambar sadarwa ta ‘yan ta’adda kuma shi ma kwararre ne akan sarrafa na’urar fashewa.
“ Bayanin kuma ya ce mai tsaron kofa ne ga shugaban ANSARU, Mohammed Usman aka Khalid Al-Bamawi. Hakazalika, shi masinja ne kuma jagorar tafiya zuwa AKIM Katibat a cikin hamadar Aljeriya da Mali. Yana aikin kafinta.
Batun ya gudu daga cibiyar gyara hali ta Kuje ranar 5 ga Yuli, 2022. A halin yanzu yana kwance a asibiti.”
A wani ci gaban kuma an bayyana shi a matsayin “babban kwamandan Daular Islama ta yammacin Afirka Okene.”
Hukumar ta ce, mutumin “ya fito fili ne a shekarar 2012 a matsayin reshen Arewa ta Tsakiya na Boko Haram.