Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta magance matsalar jinkirin samar da Farsfo sama guda 200,000 da ba a kammala ba tun bayan da ya hau kujerar mulki.
Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne yayin wani taron lacca da Access Bank ta shirya a Legas ranar Litinin, inda ya ƙara da cewa an biya bashin da ya kai Naira biliyan 28 ba tare da ƙarin kuɗi daga asusun gwamnati ba.
A cikin jawabinsa mai taken, “Dare to Dream, Dare to Innovate,” ya jaddada muhimmancin jagoranci mai hangen nesa, da sake fasalin tsari da amfani da fasaha wajen magance matsaloli.
Ya bayyana cewa amfani da sabbin dabaru da tsare-tsare ne ya ba da damar share jinkirin samar da fasfon masu yawa da kuma dawo da amincewar jama’a.
An ƙaddamar da sabbin tsare-tsaren da suka haɗa da e-visa, sabunta fasfo ba tare da zuwa ofis ga ’yan Nijeriya da ke ƙasashen waje ba, da kuma sabuwar hanyar bin diddigin fasinjoji.
Kan batun gyaran gidajen yari kuwa, ministan ya nuna damuwa kan halin da gidan gyaran hali ke ciki, inda ya bayyana cewa fiye da fursunoni 4,000 na tsare ne saboda gazawarsu na biyan tara kamar Naira 50,000.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp