Bisa ga dukkanin alamu sakin marar da aka yi wa jagoran kungiyar masu fafutikar neman kafa biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu ta zo karshe a yayin da Gwamnatin Tarayya ta nemi kotu ta soke belinsa da ta bayar a shari’ar da ake masa ta cin amanar kasa tare da wasu mukarrabansa.
Mai taimaka wa babban lauyan kasa a kan harkokin yada labaru, Malam Salihu Isah ya sanar da batun neman soke belin a wata takarda da ya raba wa manema labaru a babban birnin tarayya, Abuja da maraicen Jumar’ar nan.
Gwamnatin tarayya ta ce ta yi hakan ne a sakamakon karya ka’idodin belin da aka gindaya wa Nnamdi Kanu, a yayin da shi kuma Nnamdin yake cewa ka’idodin sun keta masa ‘yancinsa na dan adam, don haka yake fatali da su.
Galibin ‘Yan Nijeriya dai na ganin tuntuni ya kamata a ce gwamnati ta dauki mataki a kan Nnamdi Kanu a sakamakon raina kotu da nuna isa da kuma cigaba da shirya tayar da hargitsi a kasa da sunan fafutikar kafa kasar biyafara. Amma ba a yi hakan ba sai dawowar Shugaba Buhari daga jinyar da ya yi a kasar waje wanda hakan ke alamtar da cewa “kare ba ya wargi a hannun bamaguje”.