Gwamnatin Bauchi Na Shirin Warware Rawunan Wasu Hakimai

Ga dukkan alamu, rawunan wasu Hakimai da Dakatai za su warware ba da jimawa ba a Jihar Bauchi, a sakamon kaddamar da wani kwamiti da zai yi nazarin nadin da tsohuwar gwamnatin Malam Isah Yuguda ta yi musu da gwamnati mai ci ta ce an nuna danniya wurin yi.

Gwamnan Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar ya kaddamar kwamitin wanda aka dora wa nauyin nazarin yadda tsohowar gwamnatin ta kara yawan Hakimai da Dakatai daga 39 zuwa 193 ba tare da la’akari da matsin tattalin arziki ba.

Haka kuma, kwamitin zai yi dubiya kan Hakimai da Dakatan da aka dakatar domin daidaita lamarin.

Kwamitin da Gwamnan ya kafa a karkashin tsohon Alkali Dahiru Sale, zai binciki dakatarwar da aka yi wa wasu hakimai a karkashin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi a shekarar 2015.

Sanarwar da sakataren watsa labarai na Gwamnan Bauchi, Malam Abubakar Al-Sadikue ya raba wa manema labaru a Bauchi, ta ce, dakatar da Hakimai da Dakatan ya zama wajibi bisa la’akari da yadda gwamnatin da ta gabata ta kara yawansu barkatai.

Gwamnan ya yi bayanin cewar karin Hakimai da kuma Dagatan an yi su ne bisa son zuciya da kuma wariya gami da yinsu ba tare da nuna sanin ya kamata ba.

Gwamnatin ta ce tsohuwar gwamnatin kawai ta zabi wadanda take so ne ta ba su wadannan mukaman, wadda a cewarta dole ne kawai a dakatar da su domin nazari da kuma bibiyar yadda aka yi.

Gwamnan Abubakar, ya ce gwamnatinsa na matukar girmama masarautun gargajiya ba wai don kawai suna dauke da dimbin tarihi da kuma shugabanci ba, sai don su ne masu dabba’a zamantakewa da kuma al’adu kana da taimaka wa kare lafiya da dukiyar jama’ansu.

“Gwamnati ta yanke shawarar kafa kwamitin mutane masu kamala da za su duba yadda aka nada hakimai da dakatai domin fiddo wadanda suka dace domin kauce wa son kai da wariya,” a cewar Gwamnan Jihar.

Gwamnan ya kalubanci dukkanin mambobin kwamitin da su yi aikinsu tsakaninsu da Allah domin bincikowa da kuma nazarin Hakimai da Dakatan da aka dakatar domin duba matakin na gaba, sai ya ba su tabbacin cewar gwamnatin jihar za ta ba su dukkanin goyon bayan da suka dace domin su samu nasarar kammala aikinsu yadda ya dace.

Da yake jawabi a madadin kwamitin, Dahiru Sale ya sha alwashin yin aiki cikin tsoron Allah da kuma yin aiyukan da gwamnatin ta daura musu ba tare da nuna son kai ko kaucewa yin adalci ba, ya bayyana wa Gwamnan cewar zai baiwa marar da kunya wajen yin aikin da ya dace.

Sauran mambobin kwamitin dai su ne tsohon shugaban ‘yan sanda AIG Garba Mohammed (Sarkin Yakin Katagum), Ambasada Babaji Umar (Wazirin Misau), Alhaji Nuhu Mohammed Wabi (Yariman Jama’are), da kuma Alhaji Lawal Baraza (Sardaunan Dass).

Sauran su ne Alhaji Haruna Yunusa (Chiroman Ningi), Alhaji Bala Ahmed Baban Inna (Limamin Bauchi), Alhaji Bala Attahiru (Ajiyan Bauchi), Alhaji

Mohammed Gadoji (Turakin Katagum), Alhaji Abubakar Isa, Alhaji Babayo Ahmed

(Katukan Misau), Alhaji Mustapha Katagum, Alhaji Ibrahim Musa Tafawa

Balewa, sai kuma Alhaji Bashir Yakubu Lame.

Kwamitin nada makwanni biyar don su kammala dukkanin aiyukansu da kuma kawo rahotonsu wa gwamnatin jihar domin nazarin mataki na gaba.

A ranar Larabar da ta gabata ne Gwamman ya rantsar da kwamitin.

Exit mobile version