Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin a rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu, daga matakin firamare zuwa sakandare da manyan makarantu, ciki har da na jiha, na ƙasa da kuma na masu zaman kansu. Kakakin Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi, Jalaludeen Usman, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Lahadi.
Usman ya ce an yanke wannan shawarar ne bayan “tattaunawa mai zurfi” tsakaninsu da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki. Ya ƙara da cewa duk da cewa matakin ya yi nauyi, an ɗauke shi ne domin kare rayuwar ɗalibai, da malamai da ma’aikatan makarantu, tare da tabbatar da cewa yanayin karatu ya kasance cikin tsaro da kwanciyar hankali.
A cewarsa, gwamnati ta san cewar hakan na iya kawo tsaiko ga iyaye da dalibai, amma kare rayuwar yara shi ne nauyin da ya fi duk wani nauyi. Ya yi kira ga iyaye da masu makarantu da sauran jama’a su kasance masu haƙuri tare da bayar da haɗin kai, tare da tabbatar da cewa gwamnati na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro domin farfaɗo da zaman lafiya da dawo da makarantu aiki nan bada jimawa ba.
Sanarwar ta kuma tunatar da cewa jihohin Filato, da Katsina da Neja sun rufe makarantu kwanan nan saboda matsalolin tsaro, yayin da ƴan bindiga suka yi garkuwa da ɗalibai a wasu jihohi kamar Kebbi da Neja. Gwamnatin Bauchi ta ce a yanzu tilas ne a ɗauki matakin kariya kafin sake buɗe makarantu a jihar.














