Gwamnatin Jihar Kaduna ta nuna jindadi tare da yabo ga hukumar gudanarwa na ‘Arla Foods Nigeria’ a kan jarin da suka zuba na kafa kamfanin samar da madara na ‘Arla Farm project’ wanda ake sa ran zai tamaka wajen tabbatar da samun madara a Nijeriya.
Bayanin haka yana cikin jawaban da wasu manyan jami’an gwamnatin Kaduna suka yi a jawabansu daban-daban a ziyarar da suka kai kamfanin da ke garin Damau, kwanakin baya.
- Yadda Na Sha Mugun Duka A Hannun ‘Yansanda — Ajaero
- Hatsarin Kwale-Kwale: Har Yanzu Ana Neman Mutane Sama Da 70 A Taraba – NEMA
A yayin da yake maraba da tawagar jami’an gwamnatin Jihar Kaduna, Shugaban kamfanin, Peder Pedersen ya ce, ziyarar wata alama ce da ke nuna yadda gwamnatin Jihar Kaduna suka dauki masu zuba jari a jihar da muhimmanci hakan kuma zai karfafa aikin da suke yi, zai kuma kara musu kwarin gwiwa wajen bayar da nasu gudumamwar wajen bunkasar tattalin arzikin jihar da ma Nijeriya gaba daya.
A jawabinsa, kwamishinan gona na jihar Kaduna, Murtala Dabo ya nuna gamsuarsa a kan irin ci gaban da kamfanin ya samu a dan karamin lokacin da ya fara aiki, ya kuma yaba da irin kayan aikin da kamfanin ta samar, “Suna daidai da irin yadda ake tafiyar da kamfanin samar da madara a duniya’’ in ji shi.
A nata tsokacin, kwamishinar kasuwanci da kimiyya da fasaha ta jihar Kaduna, Patience Fakai, ta ce, ayyukan kamfanin zai yi matukar tasiri ga tattalin arzikin Jihar Kaduna, musamman ganin kuma zai bude kofar samar da ayyukian yi ga matasa masu yawan gaske.