Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da kashe Naira biliyan 33.45 don aiwatar da ayyukan ci gaba a faɗin jihar, musamman a fannonin gine-gine, ilimi, da lafiya, da walwalar jama’a.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai bayan zaman majalisar. A cewar wata sanarwa da Daraktan harkoki na musamman na ma’aikatar yaɗa labarai, Sani Abba Yola, ya fitar, kuɗaɗen za a rarraba su zuwa muhimman ayyuka domin inganta rayuwar al’umma.
- Kotu Ta Hana Gwamnatin Tarayya Riƙe Wa Kano Kuɗaɗen Ƙananan Hukumomi
- Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan Bashin Albashin Ma’aikatan Tsaftar Muhalli 2,369
Daga cikin kuɗaɗen, an amince da Naira miliyan 426.4 don biyan alawus na watanni tara ga masu share tituna 2,369 da aka tantance a ƙarƙashin ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi. Haka nan, Naira miliyan 109 za a kashe wajen sayo da rarraba fom din UTME/JAMB tare da horaswa ga ɗalibai a ƙarƙashin ma’aikatar Ilimi.
A bangaren lafiya, an amince da kashe Naira miliyan 284.1 don gina asibitin kiwon lafiya na zamani a Rimin Zakara, ƙaramar hukumar Ungoggo. Bugu da kari, an ware Naira miliyan 434.3 don gyaran makarantar GGSS Shekara, yayin da za a yi wa First Lady’s College, Magwan, gyara da kuɗi Naira miliyan 893.1.
Gwamnati ta kuma ware Naira biliyan 6.6 don aiwatar da ayyukan mazaɓu na 2025, tare da Naira miliyan 256.7 don gyaran ofishin Mataimakin Gwamna. Akwai kuma shirin sayen wani muhalli a Ja’en, ƙaramar hukumar Gwale, kan Naira miliyan 160, domin mayar da shi makarantar gwamnati.
A wani ɓangare, an ware Naira biliyan 5.22 don gina gidaje 1,000 masu ɗaki biyu-biyu domin raba su kyauta ga waɗanda ambaliya ta shafa. Haka nan, an amince da Naira biliyan 9.76 don gina tituna bakwai da gyaran wasu a karkara