Gwamnatin Jihar Kano, ta ayyana ranar Litinin, 23 ga watan Satumba, a matsayin ranar hutun Takutaha.
Wannan sanarwar ta fito ne daga ofishin Shugaban Ma’aikatan jihar.
- Asibitin Gombe Ya Haramtawa Ma’aikata Yin Kiripto Lokacin Aiki
- Kwalara: Kwara Ta Rufe Gine-gine 14 Saboda Rashin BanÉ—aki, Ta GargaÉ—i Masu Gidaje
A cewar sanarwar da Sakataren Ofishin, Abba Danguguwa, ya sanya wa hannu, hutun yana cikin girmama ranar bakwai ga haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).
Mutanen Kano suna bikin wannan rana a matsayin “Ranar Takutaha.”
Idan ba a manta ba Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin da ta gabata a matsayin ranar Maulidi, domin bai wa Musulmi damar murnar zagayowar ranar haihuwar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W).