Gwamnatin Jihar Kano ta fitar sanarwar umarnin haramta kafa wa, da ɗaukar aiki da gudanar da duk wata ƙungiyar Hisbah mai zaman kanta a jihar, inda ta dakatar da ƙungiyar Independent Hisbah Fisabilillahi da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ke shirin Ƙirƙirowa.
Kwamishinan yaɗa labarai ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a Kano, yana mai cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan umarnin ne domin kare zaman lafiya da kuma kare sahihancin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da doka ta kafa.
- Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano
- Ƙirƙirar Hisbah Mai Zaman Kanta: Kungiyar Lauyoyi ‘Yan Kano Ta Shigar Da Tinubu Ƙara
Umarnin ya bayyana cewa duk wani yunƙuri na ɗaukar aiki, da horarwa ko tura mutane don kafa wata Hisbah ta daban haramun ne, kuma ba shi da inganci a doka. Gwamnati ta umurci jami’an tsaro su dakatar da duk wani motsi da kuma bincikar masu ɗaukar nauyin ƙungiyar.
Gwamnatin ta kuma gargadi jama’a da su guji shiga ko tallafa wa ƙungiyar da aka haramta, tana mai cewa duk wanda ya bin umarnin zai fuskanci hukunci bisa dokokin jihar kuma umarnin ya fara aiki nan take.














