Gwamnatin Jihar Kano ta nuna damuwa game da yawaitar sata a cikin shirin bayar da magunguna kyauta, tana zargin wasu ma’aikatan lafiya da masu cin gajiyar shirin suna haɗa baki don satar magungunan da aka samar domin masu ƙaramin ƙarfi.
Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da cibiyar hulɗa da Jama’a (CCSI) ta shirya, yana mai cewa wannan matsala tana kawo cikas ga nasarar shirin.
- Kawu Sumaila Ya Yi Barazanar Maka Shugaban NNPP Na Kano A Kotu
- An Jinjinawa Kokarin Sin Na Tallafawa Ayyukan Wanzar Da Zaman Lafiya A Kasashen Afirka
Don magance matsalar, gwamnati ta fara amfani da tsarin rubutun bayanai na zamani da rajistar amfani domin tabbatar da gaskiya da adalci. Dr. Yusuf ya ce,
“Za a rubuta sunan, adireshi, da lambar waya na kowane mutum da ya karɓi waɗannan kayan, domin mu tabbatar da cewa an kai wa wadanda suka cancanta.”
Ya kuma koka kan rashin zuwa asibiti don kula da lafiya kafin haihuwa da bayan haihuwa a tsakanin mata, musamman a karkara, yana mai cewa hakan yana kara yawan mace-macen mata masu juna biyu.
Ya kara da cewa Gwamnatin Kano ta kammala wani bincike na shekara guda domin tattara bayanai kan mace-macen mata masu ciki a karkara, domin tsara matakan da za a ɗauka nan gaba.
Har ila yau, an fara gyaran cibiyoyin lafiya da ɗaukar karin ma’aikatan lafiya don samar da ingantattun wuraren haihuwa cikin aminci ga mata masu ciki.