Gwamnatin Jihar Kano ta fara rabon kayan makaranta kyauta ga ɗalibai 789,000 a makarantun firamare 7,092 da ke cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ƙaddamar da wannan shiri a ranar Litinin, inda ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na kyautata harkar ilimi a jihar. Ya ce, “Ilimi shi ne ginshiƙin gina makoma mai kyau ga yara da al’umma baki ɗaya. Wannan shiri na nuna Deuteronomy na kawar da cikas da ke hana yara zuwa makaranta.”
- Ruftawar Rijiya Yayi Sanadin Mutuwar Mutum 1 Da Jikkata 2 A Kano
- Zargin Safarar Kananan Yara: Gwamnatin Kano Ta Karbi Yara 59 Da Aka Kama A Hanyar Zuwa Nasarawa
Shugaban hukumar kula da Ilimin Bai ɗaya ta Jihar (SUBEB), Yusuf Kabir, ya bayyana yadda rabon kayan zai rage wa iyaye waɗanda ke fama da matsin tattalin arziki ƙuncin kashe kuɗi. Ya ce shirin wani mataki ne na magance matsalar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar Kano.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Ali Haruna Makoda, ya yabawa malamai bisa ƙoƙarinsu, tare da bayyana cewa rabon kayan makaranta wani ɓangare ne na sauye-sauyen ilimi. Ya ce, “Wannan shiri ya wuce batun kayan makaranta kawai; yana da nufin ba wa matasa ƙwarin gwiwa da damar samun ilimi mai inganci domin zama manyan gobe.”
Karin Hotuna
Suna Biye: