Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu a dokar da za ta wajabta yin gwaji kafin aure.
Hakan na nufin cewa dole ne daga yanzu duk wadanda ke shirin yin aure su yi gwaji.
- Kar Ku Tayar Da Hankulanku, Mun Samo Fetur Fiye Da Lita Biliyan 1.5 – NNPCL
- APC Ta Zargi Kwankwaso Da Shirya Wa Ganduje Maƙarƙashiya Kafin Zaben 2027
Wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnatin jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta ce ya zama wajibi a yi wannan doka, don rage yawan yaran da ake haifa da matsalolin rashin lafiya kamar cutar sikila, cuta mai karya garkuwar jiki da cutar hanta.
Sanrwar ta ce wanna mataki ya yi daidai da kudirin gwamnan jihar na samar da yanayi mai armashi a bangaren kiwon lafiya, da zummar rage kalubalen lafiya a jihar.
Dokar ta wajabta gwaji na cutar HIV, Hepatitis da rukunin jini na genotype, kafin aure.
Dokar ta kuma haramta wariya ko kuma tsangwamar da ake wa masu rayuwa da cutar HIV, sikila, da sauran matsaloli na rashin lafiya.