Gwamnatin jihar Kano ta rufe wasu makarantun koyar da harkokin kiwon lafiya 26 da ba su da lasisi a jihar.
A wata sanarwa da hukumar lafiya ta jihar ta aike wa manema labarai, mai dauke da sa hannun jami’ar hulda da jama’a ta ma’aikatar, Dakta Hadiza Namadi a ranar Juma’a.
- ‘Yan Bindiga Da ‘Yan Kungiyar Ansaru Sun Yi Arangama Da Juna A Kaduna
- Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rajistar Hakar Ma’adanai Ba Sai Da Katin Zabe -Babangida
Ta ce makarantun za su ci gaba da kasancewa a rufe sai bayan kammala gudanar da bincike a kansu.
Sanarwar ta kara da cewa wasu daga cikin makarantun ba su da mazauni na dindindin, sannan kuma suna koyar da wasu kwasa-kwasai da suka saba da tsarin manhajar koyar da kiwon lafiya, tare kuma da tatsar dalibai da iyayensu makudan kudade na babu gaira-babu-dalili.
A cikin sanarwa ta shawarci mazauna jihar da su guje wa irin wadannan makarantu, ta hanyar zuwa makantun da gwamnati ta bai wa lasisi.