Gwamnatin Jihar Kano ta shawarci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu gabanin hukuncin kotun daukaka kara da za a yanke a gobe Juma’a.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye, ya raba wa manema labarai a Kano a ranar Alhamis, ta hannun Sani Abba Yola, Daraktan ayyuka na musamman na ma’aikatar.
- Zargin Almundahana: Kotu Ta Bayar Da Belin Muhuyi Magaji Rimin Gado
- Kasashen Afirka Na Cin Gajiyar Aikin Zamanintar Da Aikin Gona Na Sin
Sanarwar ta bukaci al’ummar jihar su guji tada tarzoma ko kalaman da za su tada hankali kafin da kuma bayan hukuncin kotun.
Dantiye, wanda ke mayar da martani kan hukuncin zaben gwamna da za a yi gobe da kotun daukaka kara a Abuja, ya jaddada bukatar jama’a su wanzar da zaman lafiya domin ci gaban jihar da kasa baki daya.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su zage damtse wajen ganin an tabbatar da doka da oda don tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.