Gwamnatin Jihar Kano na duba yiwuwar samar da hukumar kula da magungunan gargajiya da dangoginsu.
Daraktan yada labaran Mataimakin Gwamna, Hassan Musa Fagge ya shaida wa LEADERSHIP Hausa hakan a Kano.
Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Litinin lokacin da ya karbi tawagar hukumar lafiya ta gwamnatin tarayya wadda Daraktan kula da sashin magungunan gargajiya da dangoginsa, Zainab Ujudu Sharif ta jagoranta.
Gwamnan wanda mataimakinsa, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya wakilta ya ce, Gwamnatin Jihar Kano na shirin kafa wannan sashi na ma’aikatar lafiya a cikin wani kokarinta na tabbatar da nagartar magungunan gargajiya.
Ya jadadda cewa gwamnatin Kano na kara himmatuwa wajen lura da lafiyar al’ummarta. A cewarsa, yin hakan wani kyakkyawan tunani ne na gwamnati domin kawar da baragurbi da jabun magungunan gargajiya.
Ya bukaci tawagar ta gabatar da takardun bayanai wanda zai amfani da su wajen mika rahotonsa gaban majalisar zartarwar Jihar Kano bisa bukatar samar da sashin.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin Kano a shirye take na samar da fili wanda zai saukaka shuka kusan dukkanin magungunan da ake bukata kamar tafarnuwa, albasa, citta da dai sauransu.
A nata bangaren, Zainab ta ce makasudin wannan ziyara shi ne, karfafa gwiwar gwamnatin Jihar Kano domin samar da dokar kafa hukumar tare da samar da wannan sashin a ma’aikatar lafiya, musamman saboda muhimmacinsa ga lafiyar al’umma.