Gwamantin Jihar Kogi karkashin Ma’aikatar Kula da Ma’adinai da Albarktun Kasa, ta haramta hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.
Haramcin na zuwa ne bayan da wasu mutum biyu suka mutu sakamakon ruftawar da rami ya yi da su a lokacin da suke hakar ma’adinai a yankin Ika-Ogboyaga da ke karamar hukumar Anka.
- Sojoji Sun Kashe Dan Ta’adda, Sun Kama Wasu 3 A Kaduna
- Yadda Bidiyon Tsiraicina Ya Karade Shafukan Sada Zumunta – Safara’u
Ma’aikatar ta bayar da sunayen wadanda suka mutum da Amodu da Attah.
Sannan, ta ce sun mutu ne a karshen mako lokacin da suke hako ma’adinai a cikin wani rami.
A wata sanarwar da Kwamishinan Ma’adinai da Albarktun Kasa na jihar, Injiniya Bashiru Gegu l, ya sanya wa hannu, gwamantin ta umarci dukkanin masu hakar ma’adinai da su gaggauta zuwa domin yin rijista da ma’aikatar domin samun aminci da salamar gudanar da ayyukansu.
Gwamnatin ta nuna fushinta kan wasu da ke hako .a’adinai ba bisa ka’ida ba, inda ta shawarce su da su yi rijistar domin daddale sahihancinsu da kwarewarsu a kan harkokin hako.
Sanarwar ta kara da cewa kauce wa wannan umarnin zai sanya gwamnati rufe wuraren da ake hako ma’adinai da daukar matakin kan masu hakar.
Kwamandan Hukumar Tsaron Farin Kaya ta (NSCDC), Oyinloye JK, ya ce bincike masu mallakin wurin harko ma’adinai na gudana, ya tabbatar da cewa an yi jana’izar mamatan kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.