Gwamnatin Nijeriya Ta Samu Rancen Dala Biliyan 2.5 Don Aikin Jirgin Kasa Na Legas-Ibadan

Daga Mahdi M. Muhammad

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce, Gwamnatin tarayya ta karbi rancen kusan dala biliyan biyu da rabi da ta shiga aikin gina hanyar jirgin kasa da ya hada Legas da Ibadan.
Amaechi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na ‘Channels Telebision’ na shirin ‘Newsnight’ wanda aka watsa ranar Litinin.
“Idan kuka duba duka jimillar kudin, zai kasance dala 2.5 zuwa 2.6 biliyan da muka aro daga bankin Edim na kasar sin,” inji shi.
Ministan ya bayyana cewa, shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yanke na shimfida layin dogo zuwa tashoshin jiragen ruwa na kasar nan ya kasance ne saboda fa’idojin tattalin arzikin da ke tattare da shirin.
Ya kara da cewa, “Amma a karshen yini, aikin ya ci kusan dala biliyan 2. Gwamnati na tari sama da dala miliyan 200 kacal. Muna fitar da kusan dala miliyan 700 saboda dole ne mu kare a tashar jirgin ruwa a Apapa wanda ba bangare na kirar asali ba ne.
“Don haka dole ne mu dauki layin dogo kimanin kilomita 45 daga Ebute-Metta zuwa tashar jirgin ruwan Apapa. Duk abin tare kusan dala biliyan 2 ne. Akwai karin wanda zasu kawo don hada tashar jirgin ruwan tsibirin Tincan zuwa Apapa. Hakan zai iya zama karin karin kudin da za mu aro daga gare su. Sun kuma ba mu rancen kimanin dala biliyan 1.4 na Legas zuwa Ibadan yayin da Gwamnatin tarayya ta yi tari game da dala miliyan 200 don yin dala biliyan 1.6,” inji shi.
Amaechi ya ci gaba da cewa, majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da cibiyoyin bayar da rancen guda biyu wadanda ma’aikatar Sufuri ta gabatar.
A cewarsa, gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ta ciyo bashin dala miliyan 500 don layin dogo daga Kaduna zuwa Abuja.
A cewarsa, “tun kafuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015, layin dogo ya dauke mu kusan dala biliyan 1, don haka dole ne mu fitar da sauran kudin. Lokacin da muka zo, an bar wani bangare na aikin saboda gazawar gwamnati na samar da wasu kudade. Don haka abin da gwamnati ta yi shi ne ta saki takwaran aikinta da kuma kudi don karin aikin da muke bukatar yi. Dole ne mu sayi kayayyaki don ba mu damar fara ayyukan kasuwanci. Ga Kaduna-Abuja, sun bada rancen dala miliyan 500.”

Exit mobile version