Gwamnatin Tarayya ta amince a rinka bayar da hutun haihuwa na mako biyu ga maza masu aikin gwamnati.
Shugabar ma’aikata ta gwamnatin tarayya, Dakta Folasade Yemi-Esan ce, ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin.
- Wata Mata Ta Shiga Hannu Kan Zargin Kashe Kishiyarta Da Tabarya A Bauchi
- Matasan Sin Masu Fasaha Sun Lashe Lambobin Yabo Bakwai A Gasar Duniya
Sanarwar ta ce “Gwamnati ta amince da hutun haihuwa ga ma’aikata maza wadanda matansu suka haihu na tsawon kwanakin aiki 14.”
Sanarwar ta kara da cewa ba za a iya daukar hutun fiye da sau daya ba a cikin shekaru biyu.
Har ila yau, za a iya daukar hutun ne na haihuwa hudu.
Tun a shekarar da ta gabata ne Majalisar Dokokin Nijeriya ta fara tafka muhawara kan batun bai wa ma’aikata hutun.