Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda dalibai za su samu bashi karkashin shirin da ta bullo da shi domin tallafa musu wajen gudanar da karatunsu cikin sauki.
A cewar gwamnatin tarayya, shirin zai gudana ne a zamance ba sai daliban sun sha wata wahala wajen samun wannan bashi ba.
- Kasashen Afirka 10 Da Za Su Samu Bunkasar Tattalin Arziki A 2024
- Kasashen Afirka 10 Da Za Su Samu Bunkasar Tattalin Arziki A 2024
Babban sakataren shirin bai wa dalibai bashi na kasa, Dakta Akintunde Sawyerr shi ya bayyana hakan a fadar shugaban kasa jim kadan bayan sun kammala ganawa da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya bayyana masa cewa an samu nasarar taura kudaden bai wa dalibai bashi a asusun makarantu.
Shirin zai kuma bai wa matasan Nijeriya daman samun horon sana’o’I bayan kammala makarantun gaba da sakandare.
Sawyerr ya yi wannan bayani ne ga manema labarai tare da shugaban hukumar tattara haraji ta kasa (FIRS), Dakta Zacch Adedeji.
Shi me Dakta Adedeji ya tofa albarkacin bakinsa, inda ya bayyana cewa sun gana da shugaban kasa ne saboda harajin ilimi shi ne babban hanyar samun kudin da za a bai wa dalibai bashi.
Sawyerr ya kara da cewa shirin zai taimaka wa dalibai wajen bangaren sana’ar da suke burin cimmawa, maimakon tilasta musu kan wani lamari saboda karancin kudade wajen gudanar da harkokin karatu.
Ya tabbatar da cewa shirin zai taimaka matuka gaya na hatsarin da matasan Nijeriya ke fadawa lokacin da suke yunkurin shiga kasashen Turai domin samun rayuwa mai inganci.
Sawyerr ya ce, “Mun yi tunani sosai kafin fara wannan shirin. Idan har dalibai ya bukaci wannan bashi, to ba sai ya hadu da wani mutum ba. Akwai manhaja da dalibi zai shiga wajen neman bashin.
“Ko wani dalibi da ke sha’awar amsar bashin kwai zai shiga manhajan ne sai ya cika abubuwan da ake bukata domin samun cikakken bayaninsa. Abubuwan da ake bukata sun hada da lambar jarrabawar shiga manyan makaranta da bangaren da yake karatu da kuma ranar haihuwa.
“Sauran sun hada da lambar dan kasa wanda zai tabbatar da cewa shi dan Nijeriya ne, domin bashin ana bai wa daliban Nijeriya ne kadai. Katin dan kasa zai taimaka mana wajen bayyana sahihancin bayanan dalibi. Sannan ana bukatar lambar BBN, wannan zai taimaka wajen sanin asusun dalibi.
“An kirkiri wannan shirin ne domin tallafa wa daliban Nijeriya wadanda ba za su iya biyan kudin makaranta ba, sannan kuma zai taimaka musu wajen samun sana’oin dogaro da kai.”