Gwamnatin tarayya ta janye karar da shigar a wata kotu a kan kungiyoyin kwadago na fara zanga-zanga a fadin kasar nan.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da aka aike wa manyan lauyoyin NLC, Falana da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya samu a ranar Talata a Abuja.
- Saudiyya Ta Jagoranci Zaman Sulhu Tsakanin Rasha Da Ukraine
- Alkaluman Hidimar Cinikayya Ta Yanar Gizo Na Sin Sun Karu a Watan Yuli
Wasikar mai kwanan wata 7 ga watan Agusta mai dauke da sa hannun lauyan gwamnatin tarayya, Misis B.E. Jeddy-Agba.
NAN ta ruwaito cewa Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya ta hannun Kotun Masana’antu ta Kasa (NICN) ta fitar da sanarwar sammacin shugabannin kungiyoyin kwadagon kan raina kotu tare da fara zanga-zangar.
Kungiyoyin kwadago sun yi barazanar fara yajin aikin gama-gari a fadin kasar nan daga ranar 14 ga watan Agusta, idan har gwamnatin tarayya ta gaza janye karar da ta shigar da su a kotu.
Kungiyoyin kwadagon sun gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati na cire tallafin man fetur wanda ya jefa ‘yan Nijeriya cikin kunci.
A ranar Larabar da ta gabata ne kungiyoyin suka tsunduma zanga-zangar gama gari, lamarin da ya sanya shugaba Tinubu yin zama da su tare da alkawarin kyautata rayuwar talakawa.