Gwamnatin tarayya ta jinjina wa kamfanin siminti na BUA bisa karya farashin buhun siminti daga naira 5,500 zuwa 3,500.
Da yake yaba wa kamfanin, ministan gidaje da raya birane, Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana cewa wannan shiri da aka yi zai rage tsadar siminti, wanda ke da tsada wajen gina gidaje.
- Huldar Banki Da Babu Ruwa: Bankin TAJ Ya Samu Ribar Naira Biliyan 6 A Zangon Farko
- Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Wa Matar Da ‘Yan Bindiga Suka Raba Da Muhallinta Shatara Ta Arziki
A cewarsa, zai goyi bayan ajandar Shugaba Kasa Bola Tinubu na samar da gidaje masu sauki ga ‘yan Nijeriya.
Ministan ya bayyana haka ne a matsayin martani ga sanarwar da kamfanin BUA ya bayar a ranar 1 ga Oktoba, 2023 a hukumance ta rage farashin siminti a Nijeriya.
Ya kara da cewa tsadar siminti ya haifar da tashin gwauron zabi na gidaje, wanda hakan ya sa talakawan Nijeriya ba za su iya biya ba. Ministan ya kara da cewa matakin na kamfanin BUA wani gagarumin ci gaba na saukaka kudi a kan masu neman gida.
Dangiwa ya jaddada cewa tun da ya hau kujerar minista, ya fara inganta samar da gidaje masu saukin kudi a matsayin babban abin da ya bai wa fifiko bisa tsarin ajandar shugaban kasa.
“Tashin farashin kayayyakin gine-gine, musamman siminti, ya kawo cikas ga ‘yan Nijeriya masu bukatar mallakar gidaje. Matakin da kamfanin BUA ya dauka na rage farashin siminti zuwa naira 3,500 abin yabawa ne matuka. Ya nuna fahimtar gwagwarmayar da talakawan Nijeriya ke fuskanta kuma mataki ne mai kyau na samar da gidaje mafi araha da kowa ke bukata.
“Na yaba wa kamfanin BUA saboda shawarar da ya yanke na rage farashin siminti. Matsuguni masu araha hakki ne na asali kuma wannan matakin ba shakka zai rage kalubalen da ‘yan kasar ke fuskanta. Yana nuna sadaukarwar da aka yi na inganta rayuwar al’ummarmu da kuma cimma muradin bukasa burane,” in ji shi.
Dangiwa ya bukaci sauran kamfanoni su yi koyi da BUA, inda ya bukace su da su yi la’akari da tasirin yadda wannan mataki zai bukasa rayuwar al’umma.
Ya bayyana kokarin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu wajen magance matsaloli rashin mallakar muhalli ga dukkan ‘yan Nijeriya.