Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ƙaddamar da na’urar auna masu kallo domin samar da sahihin bayanai na masu kallon talabijin a ƙasar nan.
A cikin wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga Ministan, Idris, wanda ya ƙaddamar da taron a Abuja a ranar Alhamis, ya ce na’urar tana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da cewa ayyukan watsa shirye-shirye ba wai kawai suna da tasiri ba har ma suna nuna abubuwa daban-daban da masu sauraro suka fi so kuma suke buƙata.
- Rikicin Sarautar Kano: Kallo Ya Sake Komawa Kotu
- Kamfanin Google Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Darasi 10 Kan Kirkirarriyar Basira
Ya ce: “Kayan aiki ne wanda ke ba mu ikon fahimta da kuma ba da amsa ga yanayin masu amfani da kafofin watsa labarai, samar da kyakkyawar fahimta a cikin halayen kallon su, da abubuwan da suka fi so.
“Don haka abin farin ciki ne a lura cewa a ƙarshe an samu nasara a wannan aikin da aka fara a shekarar 2020.”
Ministan ya bayyana ɓullo da na’urar a matsayin wani gagarumin cigaba da ya yi daidai da manufar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin Nijeriya ta samu cigaba da bunƙasar fasaha.
Ya ce ɓullo da na’urar ya zama dole sosai domin har yanzu Ma’aunin Masu Kallo ko Sauraro na yin amfani da tsohon tsarin Alƙalamin da Takarda na tattara bayanai kan masu kallon talabijin da masu sauraren rediyo, wanda hakan ba ya nuna haƙiƙanin abin da ko yawan mutanen da ke kallo ko sauraron wani shiri na musamman.
“Hakazalika, masu tashoshi, masu shirye-shirye, ‘yan wasa, ba su amfana ta hanyoyi da yawa; mafi muhimmanci, ba su da ƙwazo ko ƙalubalen samar da ƙarin shirye-shirye mafi kyau wanda ke biyan ‘buƙatu’, a matsayin ma’aunin wanda yake so, abin da yake so, yawan yadda yake so, da dai sauran su. Wannan ya hana ci gaban ɗaukacin harkokin nishaɗi da yaɗa labarai a Nijeriya.”
Ministan ya ce abin takaici ne ganin cewa duk da cewa ƙasar tana da yawan masu kallo sama da sau uku a Afirka ta Kudu, kuɗaɗen da ake samu a tallace-tallacen talabijin na Nijeriya ya yi kaɗan idan aka kwatanta shi da na ƙasar Afirka ta Kudu, da kuma Kenya, lamarin da ya sa dole a yi amfani da tsarin da zai tabbatar da cewa kuɗin da ake kashewa a tallace-tallace a Nijeriya ya ƙaru sosai cikin shekaru biyu masu zuwa.
Idris ya ce: “Ina da yaƙinin cewa Na’urar Auna Masu Sauraro na gaskiya kuma tabbatacce zai jawo hannun jari mai yawa a ɓangaren yaɗa labarai, da bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
“Hakan kuma zai ƙara wa Nijeriya suna a matsayin kasuwa mai ingantacciyar hanyar nazarin kafafen yaɗa labarai.”
Idris ya ce aikin wanda zai samar da ayyukan yi 500 kai-tsaye da kuma ayyuka 2,500 a fakaice an tsara shi ne don da sake farfaɗo da harkar yaɗa labarai a Nijeriya da kuma inganta shi domin tunkarar zamani domin har yanzu Gwamnatin Tarayya na kan hanyar aiwatar da Canji zuwa Dijital.
Ya nanata ƙudirin Shugaba Tinubu na bunƙasa harkar yaɗa labarai gaba ɗaya a Nijeriya kamar yadda ya bayyana a cikin umarnin da ya ba Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Saka Hannun Jari ta Tarayya da Bankin Masana’antu a kwanan baya na faɗaɗa hanyoyin hada-hadar kuɗi ga Masana’antar Watsa Labarai.
Ministan ya umarci mai ba da sabis, First Media Entertainment Integrated Limited/GARB, ya haɓaka faɗakarwar jama’a da ba da shawarwari ga duk ƙungiyoyin sashe waɗanda suka dace don yin amfani da isassun damar Na’urar Auna Masu Kallo.
Taron ya samu halartar Ministar Fasaha, Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙire-ƙirƙire, Barista Hannatu Musawa; Shugabar Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar Dattawa; Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Sanata Eze Kenneth Emeka; Shugaban Kwamitin Majalisar kan Yaɗa Labarai, Wayar da Kai, Ɗa’a da Ɗabi’u na Ƙasa, Hon. Steve Fatoba; Jakaden Bulgeriya a Nijeriya, Yanko Yordanov; tsohon Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Lai Mohammed; Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Mista Bayo Onanuga, da dukkan manyan daraktocin hukumomi a ma’aikatar da sauran manyan baƙi.