ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, June 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (1)

by Ishaq Idris Gulbi
2 years ago
Sharhi

Gabatarwa:

A jerin littattafan Adabin Zamani/Rubutaccen Adabi da Hukumar shirya jarabawa ta matakin iya karatu da rubutu don kananan Makarantun Sakandare ta fitar, don shekarar 2017 zuwa 2019 don dalibai da Hausar ce harshensu na uwa ko na farko (list of literature set books for Basic Education Certificate Edamination 2017 – 2019 Hausa L1), akwai:

ZUBE

ADVERTISEMENT

1. Sidi Ya Shiga Makaranta na Umaru Ladan da Michael Crowder da kamfanin dab’i na Jami’o’in Afirka da ke Ibadan ya wallafa a shekarar 1981.

2. Tauraruwa Mai Wutsiya na Umaru Dembo da Kamfanin dab’i na Arewa wato Northern Nigerian Publishing Company (NNPC) da ke Zariya ya wallafa a shekarar 1969.

LABARAI MASU NASABA

Super Eagles Ta Tafi Poland Domin Wasan Sada Zumunta

EFCC Ta Kama Mutum 11 Masu Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba A Kwara

  • Falalar Goman Farko Na Watan Zulhajji (2): Allah Ya Fi Son Kyawawan Ayyukan Da Aka Yi A Kwanakin
  • Falalar Goman Farko Na Watan Fahimtar Sayyidina Umar (RA) Da Sayyidina Aliyu (RA) Kan Ramakon Ramadan A Goman Zulhajji

WASAN KWAIKWAYO

1. Zaman Duniya Iyawa ne na Yusuf Ladan da kamfanin dab’i na Arewa (NNPC) da ke Zariya ya wallafa a shekarar 2004.
2. Malam Mahamman na Muhammad Bello da kamfanin dab’i na Arewa na (NNPC) da ke Zariya ya wallafa a shekarar 1981.

WAKA

1. Wakokin Hausa na Suleman Na’ibi Wali da sauransu da Kamfanin dab’i na NNPC da ke Zariya ya wallafa a shekarar 1982.

To da yake ni aka dankawa ‘yan aji daya na karamar Sakandare (JSS1) don koya musa wadannan littattafai, sai na yanke shawarar mu soma da karanta littafi na farko na zube wato Sidi Ya Shiga Makaranta.

Mun soma karanta littafin a aji tare da dalibai sai dai kamar yadda na ci karo da kurakurai a littafin wasan kwaikwayo na Kulba Na |arna na Umaru Danjuma, a shekarar bara lokacin da nake koyar da ‘yan aji daya na babbar Sakandare (SS1), har Jaridar Leadership ta Hausa ta dau mako biyu tana bugawa (28/3/2013 zuwa 4/4/2014), haka nan muka ci karo da irin wadannan kurakurai a littafin Sidi Ya Shiga Makaranta.

Kurakuran da suke cikin Sidi ya shiga Makaranta.

Littafin zube na Sidi Ya Shiga Makaranta yana da shafi tamanin da shida (86) da babi tara. Littafi ne dan karami da aka yi masa kirar saukin dauka (Nobel). Mai launin kore da zanen hoton Sidi da suma irin ta ‘yan makaranta a wadancan shekaru a bangon littafin na gaba, da hoton wani da babbar riga da doguwar hula a bayan Sidi, sai kuma ginin soraye irin na gidajen sarauta a can bayansu. Sai bangon baya na littafin inda aka yi bayanin marubutan littafin, da bayanin cewa littafin fassara ce daga littafin Sani Goes To School.

Inda ni ne zan fassara ‘Sani Goes to School’ da zan sa ‘An Sa Sani A Makaranta ko An Kai Sani Makaranta. Tunda dan makarantar Firamare dai sa shi ake yi a makaranta ba shi yake shiga makaranta da kansa ba ballantana a ce Sidi Ya Shiga Makaranta. Amma fa ra’ayina ne.
A kasan sunan littafin an rubuta marubutan wato UMARU LADAN & MICHAEL CROWDER. Gyaran a nan maimakon & da aka sa, da an sa DA. Ya zama UMARU LADAN DA MICHAEL CROWDER.

A babi na daya shafi na daya layin farko an rubuta wani ya doka sallama daga waje. Maimakon Wani ya doka sallama daga waje.

A sakin layi na uku jimlar farko an rubuta ya ji karar mota, maimakon ya ji dirin mota.

A jimla ta gaba an rubuta ba wai santin furar da ya ke sha ne kawai ba, maimakon ba wai santin furar da yake sha ce kawai ba.

Sai sakin layi na hudu inda aka rubuta kugin lanroba, maimakon dirin landiroba.

Can kusa da karshen sakin layi na hudu an rubuta ‘Ganin haka sai Sidi ya hakura da zuwa kallon motar, Ya yi ta shafa fitullun motar gaba da baya. Ya lelleka karkashin motar kamar makaniken da ke neman abin da ya lallace.

Sidi da ya hakura da zuwa ganin mota, sai kuma aka ce yana ta shafa fitullun motar? Sai kalmar MAKANIKE. Tabbas kalma ce ta aro daga Ingilishi MECHANIC. Sai dai BAKANIKE ni dai na ji Bahaushe yana cewa.

A shafi na biyu sakin layi na biyu an rubuta da idai, maimakon daidai.
Sai sakin layi na kusa da na karshe a shafin na biyu da aka rubuta in ji, maimakon In ji.

A shafi na uku sakin layi na farko an rubuta sadad da, maimakon sanar da. A sakin layi na biyu aka rubuta ya yi, maimakon Ya yi.

A sakin layi na uku cikin shafin na uku an rubuta tal kwabonsa, maimakon tal-kwabonsa. An rubuta ya ke, maimakon yake.

A karshen sakin layi na uku an rubuta wani ne, maimakon wane ne?
A shafi na hudu sakin layi na biyu an rubuta dakyau, maimakon da kyau. an rubuta ka ke maimakon kake. An rubuta tafiyad da, maimakon tafiyar da. A dai wannan shafi aka rubuta a ke, maimakon ake.

A sakin layi na uku an rubuta duk kasan nan, maimakon duk kasar nan/kasarnan kodayake akan samu naso a nan. An rubuta sa mun, maimakon samun. An rubuta ciyad da, maimakon ciyar da. An rubuta umurceni, maimakon umurce ni. An rubuta Afril, maimakon Afrilu. An rubuta faduwan ruwan farko, maimakon faduwar ruwan farko. An rubuta in haka ya faru, maimakon in haka ta faru.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa

Is’hak Idris Guibi
Malami a Sashen Harsuna na Kwalejin Kimiyya da Fasaha Ta Tarayya da ke Kaduna
[email protected]
08023703754

Sharhi
Ishaq Idris Gulbi
+ postsBio
  • Ishaq Idris Gulbi
    https://hausa.leadership.ng/author/ishaq-idris-gulbi/
    Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (4)
  • Ishaq Idris Gulbi
    https://hausa.leadership.ng/author/ishaq-idris-gulbi/
    Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (2)
  • Ishaq Idris Gulbi
    https://hausa.leadership.ng/author/ishaq-idris-gulbi/
    Al’adar Tashe A Kasar Hausa
  • Ishaq Idris Gulbi
    https://hausa.leadership.ng/author/ishaq-idris-gulbi/
    Shin Da Gaske Tashe A Kasar Hausa Na Shirin Tashi?

MASU ALAKA

Super Eagles Ta Tafi Poland Domin Wasan Sada Zumunta
Adabi

Super Eagles Ta Tafi Poland Domin Wasan Sada Zumunta

May 31, 2026
Zambar Kudi: Kotu Ta Tasa Keyar Dillalin Gidaje Zuwa Gidan Kaso
Adabi

EFCC Ta Kama Mutum 11 Masu Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba A Kwara

February 6, 2026
CGI Babandede Mai Ritaya A Mizanin Kyawawan Halaye Da Kwazon Aiki
Adabi

CGI Babandede Mai Ritaya A Mizanin Kyawawan Halaye Da Kwazon Aiki

January 30, 2026
Next Post
Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (2)

Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (2)

LABARAI MASU NASABA

An Ceto Mutane 360 Daga Hannun Boko Haram, Wasu Na Can Riƙe Wurinsu

An Ceto Mutane 360 Daga Hannun Boko Haram, Wasu Na Can Riƙe Wurinsu

June 8, 2026
Sojoji Sun Kama Mutane 5 Masu Kai Wa Ƴan Bindiga Bayanai A Neja

Sojoji Sun Kama Mutane 5 Masu Kai Wa Ƴan Bindiga Bayanai A Neja

June 7, 2026
A Ranar Wasa Kawai Ƴan Wasan Iran Zasu Na Shiga Amurka, Bayan Wasa Su Fice

A Ranar Wasa Kawai Ƴan Wasan Iran Zasu Na Shiga Amurka, Bayan Wasa Su Fice

June 7, 2026
An Tallafa Wa Waɗanda Harin Ƴan Bindiga Ya Raba Da Muhallansu A Sakkwato

An Tallafa Wa Waɗanda Harin Ƴan Bindiga Ya Raba Da Muhallansu A Sakkwato

June 7, 2026
Daliban Kasar Sin Na Rubuta Jarabawar Gaokao Ta Shekarar Bana

Daliban Kasar Sin Na Rubuta Jarabawar Gaokao Ta Shekarar Bana

June 7, 2026
NDC Za Ta Fitar Da Sunayen Ƴan Takarar Da Suka Tsallake Tantancewa Yau

NDC Za Ta Fitar Da Sunayen Ƴan Takarar Da Suka Tsallake Tantancewa Yau

June 7, 2026
Yadda Sin Da Laos Suka Daukaka Dangantakarsu Zai Amfanawa Duniya Baki Daya

Yadda Sin Da Laos Suka Daukaka Dangantakarsu Zai Amfanawa Duniya Baki Daya

June 7, 2026
Dandalin CMG Karo Na 5 Zai Bude Sabon Babin Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Dandalin CMG Karo Na 5 Zai Bude Sabon Babin Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

June 7, 2026
Ngoshe: Boko Haram Ta Saki Mata da Yara 416 da Aka Sace A Borno

Ngoshe: Boko Haram Ta Saki Mata da Yara 416 da Aka Sace A Borno

June 7, 2026
Matsalar Tsaro: Sarkin Musulmi Ya Buƙaci ‘Yansanda Su Haɗa Kai Da Sarakuna

Matsalar Tsaro: Sarkin Musulmi Ya Buƙaci ‘Yansanda Su Haɗa Kai Da Sarakuna

June 7, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.