ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Noman Rani A Jihar Neja

by Abubakar Abba
2 years ago
Neja

Ministan Albarkatun Ruwa, Farfesa Joseph Terlumun Utseb, ya kaddamar da shirin noman rani; wanda aka yi wa lakabi da ‘Rafin-Yashi’.

Haka zalika, shirin ya kunshi samar da kadadar noma sama da guda 28 da kuma  gonar Songhai da ke karkashin hukumar kula da kogin Neja, domin kara habaka noman rani tare da lalubo  mafita a kan karancin abinci a fadin wannan kasa baki-daya.

  • NPA Ta Gargadi Masu Jibge Kwantaina Ba Bisa Ka’ida Ba
  • Gwamnatin Kano Ta Dawo Da Ma’aikatan Da Ta Dakatar Da Ganduje Ya Ɗauka Aiki

Sannan Minsitan, ya kaddamar da tankunan ruwa sama da 700,000, wadanda za a iya adanawa tare da yin tanadin ruwa domin yin noman rani.

ADVERTISEMENT

A cewar tasa, “daya daga cikin tankunan ruwan; za su rika yin amfani da shi wajen tura ruwa zuwa Rafin-Yashi, domin aiwatar da noman rani, inda sauran kuma za a rika amfani da su wajen tura ruwa zuwa gonar Songhai.

Har ila yau, Dam din Rafin Yashi, wanda guda ne cikin ayyukan da ministan ya kaddamar, ya kai zurfin kimanin kafa 650,000, wanda ko shakka babu zai yi matukar taimakawa; wajen rage ambaliyar ruwan sama a tsakanin al’ummar da ke zaune kusa da Dam din na Rafin Yashi,” in ji shi.

LABARAI MASU NASABA

An Horas Da Masu Kiwon Dabbobi Dabarun Kiwon Zamani

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa

Ministan ya kara da cewa, idan aka kammala aikin wannan Dam, zai taimaka wajen samar da wutar lantarki da noman rani tare da taimakawa wajen kirkiro da ayyuakan yi da farfado da tattalin arzikin wannan kasa da kuma habaka samar da wadataccen abin abinci, wanda hakan ya yi daidai da kudire-kudiren Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Bugu da kari, ya sanar da cewa, a makon da ya gabata; ma’aikatarsa ta kaddamar da ayyukan noman rani na shekarar 2023, domin bunkasa samar da wadataccen abinci  a fadin kasar.

Ministan ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Neja, ta samar da wadatacciyar kasa a Hukumar Kula da Kogin Neja, domin a rika yin noman rani, don amfanin jihar da kuma kasa baki-daya

Kazalika, ya sanar da cewa; akwai bukatar Gwamnatin Jihar ta samar da kayan aikin noman rani tare da bai wa ‘yan jihar kwarin guiwar rungumar yin ayyukan na noman rani, a cewar tasa wannan hanyar ce kadai za a kara samar da wadataccen abinci a fadin dukkanin wannan kasa.

Har wa yau ya kara da cewa, dole ne a samar da wadataccen abinci ga kafatanin ‘yan Nijeriya da kuma wanda za a rika fitarwa zuwa kasashen ketare.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Abubuwa Biyar Game Da Kiwon Talotalo
Noma Da Kiwo

An Horas Da Masu Kiwon Dabbobi Dabarun Kiwon Zamani

December 20, 2025
Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa
Noma Da Kiwo

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Yaba Da Tsarin Aikin Noma Na Jihar Jigawa

December 19, 2025
Kiwon Dabbobi Da Fasahar Kimiyyar Zaman
Noma Da Kiwo

Kiwon Dabbobi Da Fasahar Kimiyyar Zaman

December 14, 2025
Next Post
Yadda Ake Hada Turaren Hammata

Yadda Ake Hada Turaren Hammata

LABARAI MASU NASABA

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.