Hukumar da ke kula da wutar lantarki a Nijeriya (NERC) ya amince da karin kudin kudin wutar lantarki tun daga ranar 1 ga watan Junairun shekarar 2021. A yan masu amfani da wutar lantarki za su biya sabon farashi ga kamfanonin rarraba wutar lantarkin (DISCO). Wannan ya zo a wata biyu bayab an tilasta wa hukumar amincewa da karin kudin wutar lantarki ga ’yan Nijeriya tun daga watan Nuwambar shekarar 2020.
Sanarwar karin wanda sabon shugaban hukumar NERC, Injiniya Sanusi Garba ya rattaba hannu a ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2020, sabon karin biyan kudin wutan lantarki zai fara aiki a ranar 1 ga watan Junairun shekarar 2021, kamar yadda dokar hukumar mai lamba ta NERC/2028/2020 ta amince da hakan.
A cikin Sabuwar dokar hukumar mai lamba NERC/225/2020, hukumar NERC ta bayyana cewa, ta dauki wannan mataki ne saboda an samu hauhawar farashin kayayyaki a cikin watan Nuwambar shekarar 2020, sannan kowacce dala daya tana kan naira 379.4 a watan Disambar shekarar 2020, sakamakon haka, dole ne kamfanonin wutar lantarki su kara farashin kudin wutar lantarki. Wannan sabon karin farashin wutar lantarki zai ci gaba da zama a haka har sai zuwa watan Yunin shekarar 2021 lokacin ne saka sake duba wani sabon tsari wanda za a yi amfani da shi har zuwa watan Disambar shekarar 2021, hukumar NERC ta bayyana wannan bayanai.
Tun daga farkon watan Disambar shekarar 2020, hukumar NERC ta fara bibiyan sabon farashin karin kudin wutar lantarki wanda ta samu nasarar kammalawa a ranar 1 ga watan Junairun shekarar 2021. Hukumar NERC ta kara wa kamfanonin rarraba wutar lantarki kudade a watan Satumba, amma an samu nasarar dakatar da lamarin sakamakon cimma yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadugo wanda aka bi hanyar tattaunawa a tsakani. Bayan haka, a ranar 1 ga watan Nuwambar shekarar 2020, wa’adin dakatar da karin wutar lantarki ya cika bayan an yi wa masu amfanin da wutar lantarki ragi wadanda ba sa samun wutan lantarki na awa 12 a kullum.