Gwamnatin tarayya ta shigar da karar kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC a gaban kotu bisa zarginsu da bijirewa umarnin hana kungiyoyin shiga harkar masana’antu.
An gabatar da “sanarwar rashin biyayya ga umarnin kotu” wanda kuma ake kira “sashe 48” a gaban kotun masana’antu ta kasa da ke Abuja ranar Laraba.
- Ƙarfin Soja Ne Matakin Da Za A Dauka A Kan Nijar -Sojojin ECOWAS
- Cire Tallafin Fetur: Gwamnatin Zamfara Ta Amince Da Raba Kayan Abinci Don Tallafawa
A ranar Laraba ne kungiyoyin suka shiga yajin aiki da kuma zanga-zanga don nuna kin amincewa da cire tallafin man fetur da gwamnatin shugaba Tinubu ta yi.
NLC da TUC sun koka kan halin matsin rayuwa da tashin farashin kayan masarufi da cire tallafin man fetur din ya hafair.