Gwamnatin tarayya a ranar Larabar da ta gabata ta ce fifikon da gwamnonin jihohi ke nunawa na gina gadar sama da filayen jiragen sama a maimakon ayyukan da za su inganta rayuwa a yankunan karkara ba ya taimaka wa shirye-shiryenta na rage radadin talauci a kasar nan.
Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Clement Agba ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa wata tambaya bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya shaida wa manema labarai cewa kashi 72 cikin 100 na talaucin da ake fama da shi a Nijeriya ana samunsa ne a yankunan karkara, wanda ya ce gwamnonin jihohi ne suka maida su saniyar ware.
Agba, ya ce gwamnatin tarayya a nata bangaren ta yi iya bakin kokarinta wajen rage radadin talauci, ya kara da cewa fifikon da gwamnonin ke baiwa birane sama da karkara ke sa mutanan karkara basa amfana da shirin gwamnatin tarayya na rage radadin talauci.
Ya ce gwamnonin sun mayar da hankali ne wajen gina gadar sama da filayen saukar jiragen sama da sauran ayyuka da ake iya gani a manyan biranen jihohin maimakon saka hannun jari a fannonin da ke inganta rayuwar al’umma kai tsaye a yankunan karkara.
Ya shawarci gwamnoni da su mai da hankali kan ayyukan da za su iya fitar da mafi yawan jama’a daga kangin talauci.