An gudanar da shirye-shirye na musammam na CMG a kasashen Spaniya da Brazil, wadanda ke zaman somin-tabi na shagalin murnar Bikin Bazara, a biranen Madrid da Sao Paulo. Mataimakin darektan sashen wayar da kan al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya gabatar da jawabi ta bidiyo.
Cikin jawabin, Shen Haixiong ya ce Bikin Bazara ba hutu ne da MDD ta ayyana kadai ba, ya kuma shiga cikin jerin al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba da dan adam ya gada a bara. Ya ce an shafe shekaru 42 jere ana gudanar da shagalin Bikin Bazara na CCTV, kuma ya zama wani shirin talabijin na gargajiya da fasaha da aka fi kallo a duniya. Ya ce suna gayyatar masu kallo na duniya su shiga wannan katafaren shagalin, domin Sinawa dake nesa da gida su ji tamkar suna gida, haka kuma abokai dake kasashen waje su yayata wannan biki na gargajiya mai sigar Sin. (Fa’iza Mustapha)