Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin da Talata 26 da 27 ga watan Disamba 2022 da kuma Litinin 2 ga watan Junairu a matsayin ranakun hutun bukukuwan Kirsimeti da ranar Dambe da sabuwar shekara.
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hutun ga ‘Yan Nijeriya a madadin gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, ya muma taya mabiya addinin kirista da sauran ‘yan Nijeriya mazauna gida da na kasashen waje murnar bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara ta bana.
- Matsalolin Da Kirsimetin Bana Ke Fuskanta
- Kirsimeti: Wata Musulma Ta Raba Wa Mata 50 Kiristoci Kayan Abinci, Atamfofi Da KuÉ—i A Kaduna
Aregbesola ya hori Kiristoci da su yi koyi da Yesu Kiristi a cikin ayyuka da kuma bin koyarwarsa, musamman a kan bin gaskiya da zumunci da ƙaunar juna.
Aregbesola ya kuma tabbatar wa da ‘Yan Nijeriya cewa, gwamnati ta samar da ingantattun matakai don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, kuma yana sa ran ‘yan Nijeriya za su tallafa wa kokarin hukumomin tsaro ta hanyar samar da bayanai masu amfani da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.
Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su kasance masu lura da tsaro, inda ya bukaci da su kai rahoton duk wani mutum ko wani abu da basu gamsu da su ba ga hukumar tsaro mafi kusa da su.